Dalilin Da Ya Sa Saudiyya Ta Rage Adadin Mahajjatan Najeriya

[ad_1]

A bana maniyata 50,000 ne za su yi aikin Hajjin bana, sabanin dubu chasa’in da biyar, kuma tuni har an riga an kwashe alhazai dubu goma sha daya da dari hudu, wadanda a bana suna sauka a birnin Madina ne kai tsaye.

Shugaban hukumar Alhazai na kasa, Barr. Abdullahi Muktahar, ya ce rage yawan alhazan da aka yi, ya biyo bayan wani matakin aiki ne da hukumomin Saudiyya suka gindaya.

Daga cikin ka’idojin da suka gindaya, hukumomin na Saudiyya sun ce sun dauki wannan mataki ne domin sanin yawan bakin da za su je kasar don yi musu tanadi.

Sai dai kuma a Najeriya, bayanai sun nuna cewa sai makonnin biyun karshe da za a rufe filin jirgin sama ne wasu mutane ke biyan kudinsu na zuwa Makka.

Barr. Abdullahi ya yi kira ga masu kula da ayyukan hajji da masu ruwa da tsaki, da cewa ka da su bari masu suka su karkatar da hankalinsu.

Ya kara da cewa bin ka’idoji da dokokin da aka gindaya, musamman don gudanar da ayyuka cikin nasara, na da matukar muhimmanci.

Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda:

[ad_2]

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da kisan kai da fashi da makami a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce a cikin mako guda  jami'an ta sun kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata fashi...

Ƴan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Gyaran Hali na Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami'an ta sun kama Kyari Kur ɗaya daga cikin ɗaurarrun da suka tsere daga gidan gyaran hali ...

Ƴansanda sun kama mutumin da yake lalata da ƴar cikinsa

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama Ibrahim Aliu mai shekaru 41 a duniya a Papa Olosun, Oja Odan a karamar hukumar Yewa...

Majalisar wakilai za ta samar da jami’ar Bola Ahmad Tinubu

Ƙudurin kafa dokar kafa Jami'ar Karatun Yaruka Ta Bola Ahmad Tinubu ya tsallake karatun farko a majalisar wakilai ta tarayya. Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu...