Dalilan da suka jawo tsada da karancin Gas ɗin girki

Ana cigaba da fuskantar karanci tare da tashin farashin iskar gas a garuruwa daban daban dake sassan Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa ana fuskantar karancin iskar din girki a jihohi irinsu Lagos, Kano, Maiduguri da sauransu kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya gano.

Manyan dillalan gas sun bada tabbacin cewa karancin da aka samu na wucin gadi ne kuma zai zo ƙarshe nan bada jimawa ba.

Shugaban kungiyar NALGAM ta ƴan kasuwa masu sayar da man iskar gas, Oladapo Olatunbosun ya ce an samu ƙarancin ne sakamakon lalacewar wani jirgin ruwa a teku dake ɗauke da iskar gas tan 14000 akan hanyarsa ta zuwa Lagos.

Ya kara da cewa da zarar jirgin ya iso Lagos za a samu wadatar iskar gas.

More from this stream

Recomended