City ta kai wasan karshe a kofin FA

Man City

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Fatan Manchester City na lashe kofi hudu a bana na kara tabbata, bayan da ta samu nasara a wasan dab da na kusa da na karshe da ta kara da Brighton ranar Asabar a filin wasa na Wembley.

Kungiyar ta samu nasara ne da ci daya mai ban haushi, ta hannun Gabriel Jesus wanda ya daga ragar Brighton a minti na hudu da take wasa.

A yanzu dai kungiyar wadda ita ce ta lashe kofin Premier League na bara, tana ta biyu a kan teburin Premier da tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool wacce ke mataki na daya, inda kuma take da kwantan wasa daya.

Tuni dai kungiyar ta Etihad ta lashe kofin Caraboa na bana, bayan da ta yi nasara a kan Chelsea a bugun finariti.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...