Champions League: ‘Yan wasan Madrid da za su tafi Ajax

Real Madrid

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Real Madrid za ta tafi Ajax a wasan farko zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da za su kara a ranar Laraba.

A Champions League takwas da suka buga, Real ta yi nasara a karawa shida, Ajax ta ci wasa biyu.

Sun kuma buga European Cup hudu, inda Ajax ta ci wasa biyu, Real ta yi nasara a daya da kunnen doki a fafatawa daya.

Real Madrid tana da kofin Zakarun Turai na Champions League guda 13, ita kuwa Ajax tana da shi hudu.

‘Yan wasan Real Madrid:

  • Masu tsaron raga: Navas da Courtois da kuma Altube.
  • Masu tsaron baya: Carvajal da Vallejo da Ramos da Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma Reguilón.
  • Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da Asensio da Brahim da kuma Ceballos.
  • Masu cin kwallo: Mariano da Benzema da Bale da Lucas Vázquez da kuma Vinicius Jr.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...