CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.

Babban bankin ya bayyana hakan ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan Mayu 6, 2024, mai dauke da sa hannun Daraktan sa ido kan harkokin bankuna, Adetona Adedeji.

Abokan ciniki na wasu Bankunan sun nuna damuwarsu kan yadda bankunan suka fara tattara kudaden  ajiya na tsabar kudi tun daga ranar 1 ga Mayu.

Manema labarai sun ga haka ne a wani sakon imel da daya daga cikin kwastomomin bankin ya tura.

Dangane da matakin da bankin ya dauka, kashi biyu cikin 100 na kudaden ajiya sama da N500,000 za a cire ga daidaikun mutane, yayin da masu rike da asusu na kamfanoni kuma za a caje su kashi biyu bisa dari akan ajiya sama da N3m.

More from this stream

Recomended