‘Buhari ba zai tsoma baki a zaben jihohi ba’

Za a sake zaben gwamna a wasu mazabu na jihohin Najeriya da aka soke zabensu

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Yayin da a Najeriya lokutan zaben cike gibi ke kara matsowa, bayan zaben gwamnonin da hukumar zaben kasar ta ce ba su kammalu ba, fadar shugaban kasar ta yi jan kunne ga magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki kan cewa ba za ta tsoma baki cikin sakamakon zabukan ba.

Hukumar zaben ta Najeriya dai ta tsayar da ranar 23 ga watan Maris ne a matsayin ranar da za a kammala zabuka a jihohin kasar biyar, wato Kano, da Plateau, da Adamawa, da Sokoto, da kuma Benue.

A cikin wata takarda ta hannun mai bai wa shugaban kasar shawara kan yada labaru Garba Shehu, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce hukumar INEC ita ce ke da wuka da nama a kan duk wani zabe da za a gudanar.

Sanarwar ta kuma yi suka game da masu ganin laifin shugaban kasar saboda rashin nuna ko-in-kula a kan zabukan da za a kammala a jihohin.

Inda sanarwar ta zargi wasu ‘yayan jam’iyyar APC mai mulkin kasar da kokarin ganin shugaban kasar ya yi amfani da karfinsa wajen murde sakamakon zaben.

Sai dai mai magana da yawun nasa, a cikin sanarwar ya ce kundin tsarin mulki bai ba wa shugaba Muhammadu Buhari ikon tsoma baki cikin harkar zaben kasar ba, saboda haka ba zai yi abinda ya karya tanade-tanaden kudin tsarin mulkin kasar ba.

Ya kuma kara da cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, na cin gashin kanta ne, kuma za ta ci gaba da aikinta ba tare da tsoma bakin shugaban kasar ba.

A cikin jihohi biyar da za a gudanar da zaben cike gibi na zaben gwamnonin kasar, a jihar Plateau ce kawai jam’iyyar APC mai mulkin kasar ke kan gaba a yawan kari’u. Inda take da kuri’a 562,109, yayin da jam’iyyar PDP mai hamayya ke da kuria’a 559,437.

A sauran jihohin kuwa jam’iyyar PDP ce ke da rinjaye a yawan kuri’a.

Bayan gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 29 na kasar, a ranar 9 ga watan Maris din shekara ta 2019, jam’iyyar APC ta lashe zabe a jihohi 13, yayin da PDP ke da jihohi 9.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...