Brexit: Majalisa to Yi fatali da Daftarin Therasa May

Theresa May ta shiga tsaka mai wuya

Hakkin mallakar hoto
UK PARLIAMENT/MARK DUFFY

Image caption

Theresa May ta shiga tsaka mai wuya

Donald Tusk, Shugaban kungiyar Tarayyar Turai, ya shawarci Birtaniya da ta ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar, bayan majalisar kasar ta yi watsi da daftarin Firaminista Theresa May na ficewa daga Turai.

A wani sako twitter da ya wallafa mista Tusk ya ce idan yarjejeniya taki samuwa, kuma babu wanda ya ke son ganin an cimma daidaituwa, to wane ne ya ke da zuciyar cewa ga shawara takamaimai.

‘Yan majalisa 432 ne suka jefa kuri’a kin amincewa da daftarin, yayin da 202 suka yi na’am dashi. Tuni dai Jami’ai a Turai da ‘yan siyasa suka soma nuna rashin jindadinsu da sakamakon.

Wannan ya kasance gagarumin kaye irinsa mafi girma da wata gwamnatin Burtaniya mai ci ke fuskanta a tarihi, inda kuri’u 118 na adawa ya fito daga bangaren jam’iyyar Conservative ta firaminista Theresa May.

Sakamakon zaben ya haifar da kokwanto a zukatan masu fatan ganin lallai Burtaniya ta raba gari da Tarayyar Turai, kuma shugaban jam’iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn ya bijiro da batun jefa kuri’ar yanke kauna ga gwamnatin Misis May.

Hakazalika sakon twitter Mista Tusk, na cigaba da jan hankali yayin da wasu ke tafka muhawara kan mokar kasar a sassan Turai.

A nashi martanin shugaban hukumar tarayyar Turai Jean Claude Juncker ya gargadi cewa lokaci na kurewa Burtaniya na iya cimma wata yarjejeniyar.

Shi kuwa Babban jami’in da ke shiga tsakanin na kungiyar Tarayyar Turai kan ficewar Burtaniyar daga kungiyar, Michel Barnier ya ce lokaci ne da ya kamata gwamnatin Burtaniya ta fito ta bayyana takamaiman matakin da za ta dauka, domin kawunan kungiyar zai cigaba da kasancewa a hade da jajircewa wajen neman daidaituwa.

Tuni dai suma kasashen Jamus da Faransa da Ireland suka mayar da martanin nuna rashin jindadinsu tare da fargabar yanayin da turai za ta iya tsintar kanta muddin abubuwa suka gaggara daidaituwa.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...