Boko Haram Ta Kai Hari A Kan Sojojin Najeriya A Kusa Da Maiduguri

Wannan harn dai yasa mazauna wannan kauyukan arcewa daga gidajensu zuwa cikin daji dan gudun abin da zai kai ya komo, yayinda aka ce jami’an sojan sun yiwa mahara ba dadi, inda aka ce sun yi shigar burtu irin na sojan suka kuma soma buda wuta kan jami’an sojan, suma jami’an sojan sun maida masu da martani suka kuma ci galaba a kan maharan.

Haka zalika wannan harin ya rutsa da wasu matafiya dake bin wannan hanyar kamar wani da wannan hari ya rutsa da shi a kan hanyarsa na dawowa daga sayan icce a garin na Auno ya yiwa wakilin Muryar Amurka bayani ta wayar tarho. Mutumin yace yanzu haka kowa na ta kansa ne ya tsira da rayuwarsa.

Wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda ya ci gaba da tattaunawa da wasu da suka arce suka buya a ciki daji bayan wasu sun fada masa bindiga ta kama wani kuma tuni an kai shi asibiti. Wani da ya gudu da ransa ya shaida mana cewa maharan da sojojin sun yi bata kashi kuma haka ne ya yi sanadiyar mazauna kauyen suka shiga daji.

Wannan lamari yana aukuwa ne a daidai lokacin da wani kwamiti mai karfin gaske karkshin jagorancin gwamnan jihar Borno Ukasha Shattima uka aikawa shugaba Muhammadu Buhari rahoto a kan halin da ake ciki game da tsaron jihar Borno.

Ga rahoton da Haruna Dauda ya aiko mana daga Maiduguri:

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...