Boko Haram ta hallaka mutum 11 a Maiduguri

'Yan sanadan kwantar da tarzoma a Najeriya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan sanda a birnin Maiduguri a jihar Borno a Najeriya sun tabbatar da cewa kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane 11 da kuma raunata wasu 15.

Wani shugaban kungiyar mayakan sa-kai ya bayyana cewa an kai harin ne da nufin dakatar da mutane zuwa rumfunan zabe.

Harin ya faru ne da safiyar Asabar a kudancin birnin, inda mayakan suka bude wuta, wasu ‘yan kunar bakin-wake kuma suka tarwatsa kansu da bama-bamai.

A yau ne aka shirya gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar, sai dai an dage zaben zuwa mako mai zuwa sa’o’i kadan kafin a fara kada kuri’a.

Aikace-aikacen ‘yan ta’adda ya tilasta wa mutane da dama barin muhallansu a Borno, al’amarin da ya jawo hukumar zabe ta kirkiri rumfunan zabe a sansanonin ‘yan gudn hijira.

Ko a ranar Laraba da ta gabata ‘yan Boko Haram sun far wa ayarin motocin gwamnan Borno, inda suka kashe mutum uku.

More News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...

Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...