Connect with us

Hausa

Kasuwar ‘yan kwallon kafa: Makomar Messi, Lamptey, Chukwueze, Alli, da Nunez

Published

on

Lionel Messi

Manchester City ta ce a shirye ta ke ta biya ‘yan wasanta Raheem Sterling mai shekara 25 da Kevin de Bruyne mai shekara 29 albashin da yafi na kowane dan wasa a Gasar Firimiyar Ingila. (90 Min)

Atletico Josep Maria Bartomeuta bi sahun Bayern Munich da Sevilla wajen sa ido kan dan wasan baya na Brighton mai suna Tariq Lamptey, dan wasa mai shekara 20. (Mail)

Man Utd da Leicester da Everton na sha’awar dan wasa Samuel Chukwueze dan Najeriya mai shekara 21. (90 Min)

Paris St-Germain na son ganin Dele Alli dan wasan Tottenham mai shekara 24 ya koma can a Janairu. Kungiyar ta Faransa ta yi kokarin sayensa a bara har sau uku. (Mail)

Barcelona ta kara kaimin sayo dan wasan Uruguay da Benfica Darwin Nunez mai shekara 21 domin ya maye gurbin Luiz Suarez wanda ya koma Atletico a watan Satumba. (ESPN)

Barcelona za ta sake yin tayin sayo dan wasan Manchester City da Spaniya Eric Garci a watan Janairu. Dan wasan mai shekara 19 kwantiraginsa za ta kare a karshen kakar wasa ta bana . (Mirror)

Ajiye aikin da Josep Maria Bartomeu yayi daga mukamin shugaban kungiyar kwallo ta Barcelona na iya dagula lamura ga yunkurin komawar Garcia can a watan Janairu. (Marca)

Paris StGermain ta so sayen Thiago Alcantar mai shekara 29 amma sai suka sayo dan uwansa Rafinha mai shekara 27 bayan da dan wasan Spaniyar ya koma Liverpool daga Bayern Munich. (France Football)

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending