Connect with us

Education

Ba zamu koma koyarwa ba har sai an biya mana bukatunmu — ASUU

Published

on

Jami'a

Shugaban majalisar dattijai a Nijeriya ya roƙi malaman jami’o’i su janye yajin aikin da suke yi, su koma su buɗe makarantu don ci gaba da karantarwa.

Sanata Ahmed Lawan, ya yi wannan kira ne yayin wani taro da shugabancin ƙungiyar ta ASUU kan batutuwan da suka danganci yarjejeniyar da malaman jami’o’in suka cimma da gwamnatin tarayya.

Tun da farko, Ƙungiyar malaman jami’o’in ta ce ba za ta bi umarnin gwamnati na bude makarantun da suka shafe sama da wata shida a rufe ba.

Farfesa Haruna Musa shi ne shugaban ASUU reshen jami’ar Bayero Kano, kuma a baya-bayan nan ya shaida wa BBC irin buƙatun da ƙungiyar ke son a biya mata kafin komawa bakin aiki.

Farfesan ya ce sun jima suna yarjejeniya da gwamnatin tarayya a kan bukatun da suke son a biya musu, amma kuma shiru.

Ya ce,”Abubuwan da suke cikin yarjejeniyoyin da suka cimma da gwamnatin, abubuwa ne wadanda idan aka bisu ko shakka ba bu jami’oin kasar za su dawo hayyacinsu”.

Shugaban kungiyar ta ASUU reshen jami’ar Bayero Kano, ya ce daga cikin abubuwan akwai;

  • Samar da wadatattun kudi wanda za ayi ayyuka domin farfado da jami’oi
  • Da biyan alawus na malamai wanda ya taru har ya kai shekara biyar zuwa shida ba a biya ba
  • Da matsalar yadda jihohi ke kirkirar jami’oi barkatai ba tare da yi musu tanadi na wadatattun kudade ba domin tafiyar da su
  • Akwai batun samar da wani kwamiti da zai rika ziyartar jami’oin gwamnatin tarayyar domin ganin irin ayyukan da suke yi don gano nasarori da ma matsaloli da aka samu
  • Da kuma batun sabon tsarin biyan albashi na bai daya da gwamnati ta bullo da shi na IPPIS wanda shima ya zamo matsala babba

Farfesa Haruna Musa, ya ce batun tsarin biyan albashin nan na bai daya wato IPPIS, ya zamo mana wata matsala babba, wadda idan har gwamnati bata yi wani abu a kai ba, to malaman jami’oi ba zasu janye yajin aiki ba.

Ya ce,”Mu aikinmu ba irin na ma’ikata masu zama a ofis bane, mu aikinmu na da tanade-tanade na musamman wanda IPPIS ba zai iya magance su ba”.

Malamin jami’ar ya ce shi kansa IPPIS, ya sabawa dokar data kafa jami’oi ta Najeriya ta shekarar 2003.

Ya ce, game da batun wai an biyasu wasu kudade, sam ba gaskiya bane, domin a yanzu haka malaman jami’a na bin albashi na wata uku zuwa hudu, haka kawai wasu jami’oin ma da ke bin albashin wata shida zuwa bakwai.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending