Connect with us

Hausa

Smart Adeyemi: Ɗan majalisar dattawan Najeriya na so a riƙa yanke hannun masu cin hanci

Published

on

Sanata Smart Adeyemi

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sufurin jiragen sama a majalisar dattawan Najeriya Sanata Smart Adeyemiya, ya ce ya kammala shirye-shirye don gabatar da wani ƙudurin doka gaban zauren majalisar don yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

A cewarsa, ƙudurin dokar zai ƙunshi tsarin shari’ar musulunci da na kirista, kuma idan ta tabbata, za ta ba da damar yanke hannu ga masu aikata cin hanci da satar dukiyar jama’a ba tare da la’akari da matsayinsu ba.

A wata hira da ya yi da BBC, sanatan ya ce, a Najeriya idan aka kama mutum ya saci kudin gwamnati to ba a kama su ayi musu hukuncin da ya dace, sai aja shekaru wai ana shari’a daga bisani maganar ta sha ruwa.

Ya ce,”Shari’ar da ni nake so kuma zan gabatar da kuduri a kanta a gaban majalisarmu ita ce duk wanda ya ci kudin gwamnati aka kuma kama shi to ya kamata a hukunta shi, ma’ana ko alkali ya kwatanta yaga idan yakamata a yankewa mutum hannu to sai a yanke, idan kuma bai kai haka ba to sai a tanadi hukunci na kai mutum gona ya yi ta aiki a can”.

Sanata Adeyemi, ya ce “Idan ana bayar da irin wannan hukunci na aiki mai wahala ko yanke hannun masu kwasar kudin gwamnati, to mutane zasu shiga taitayinsu’.

Dan Majalisar dattawan, yace idan har ba a sanya dokar da zata sa mutane suji tsoro cin kudin gwamnati ba, to ba za a taba samun wani ci gaba a Najeriya ba.

Ya ce,”Amma idan aka sanya dokar da mutum zai san ko a yanke masa hannu ko kuma ya shafe shekara biyu yana noma idan ya saci kudin gwamnati, to wallahi mutane zasu daina’.

Sanata Adeyemi, yace irin wannan hukunci ba a shari’ar musulunci kawai ake yinsa ba, akwai shi a cikin Bibble.

Dan majalisar dattawan ya ce, ba zasu tsaya suna kallo wasu na cinye kudin gwamnati ba, saboda da irin wadannan kudadene ake gina ababen more rayuwa kamar asibitoci da tituna da makarantu da dai sauransu ga al’umma.

Sanatan ya ce,”Sai kaji mutum ya kwashe biliyoyin kudin gwamnati, to me ya rage, ai gara a hukunta mutum a dan rage masa hannunsa ma’ana a yanke masa hannu ta yadda idan wani gani ba zai kwatanta ba”.

Idan Allah ya yarda kafin karshen shekarar nan nake so na gabatar da kudurin wannan doka a gaban majalisarmu, domin idan har ana so a samu ci gaba a kasa dole ayi doka a kan masu cinye kudin gwamnati, don haka ya rage ruwan ‘yan majalisarmu suyi abin da ya dace kan wannan kuduri, don ni na fita da zarar na gabatar, inji sanata Adeyemi.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending