Connect with us

Hausa

Kada cutar korona ta razana ku -— Trump

Published

on

Trump

Shugaba Donald Trump na Amurka ya koma Fadar White House bayan ya bar asibiti inda yake jinyar cutar korona.

Bayan komawarsa, ya cire takunkumi, sannan ya dauki hotuna a gaban wasu tutoci a barandar Truman.

Ya bayyana kamar baya iya numfashi sosai, sai dai duk da haka ya ci gaba da nadar bidiyon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, in da a ciki yake kira ga ‘yan kasar da kada su ji tsoron cutar korona.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Democrat Joe Biden, ya ce shugaban ne ya jawa kansa, la’akari da yadda ya rika sukar masu sanya takunkumi.

Fadar White House ta sanar da cewa an kai Donald Trump asibiti kasa da sa’a 24 bayan ya kamu da cutar korona.

Mista Trump ya fara nuna alamun kamuwa da cutar ta Covid-19 ne ranar Alhamis bayan da ya sanar da cewa shi da matarsa sun killace kansu cikin daren Laraba.

An ba shi wasu magunguna, kamar yadda likitocinsa suka ce “domin samar da matakin rigakafi” a matakin farko..

Daga bisani fadar White House ta rika wallafa hotunan shugaban da ke nuna yana murmurewa, sai dai wasu rahotanni sun ce sai da aka tallafa masa da naurar taimakawa numfashi a wadansu ranaku.

Shugaban dai ya ce yana jin karfi a jikinsa sosai, sannan yana jin cewa ya ma fi lafiya a yanzu, idan aka kwatanta da shekaru 20 da suka gabata.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending