Connect with us

Hausa

Real Madrid da Valladolid: Ko Real Madrid za ta hada maki uku kuwa? | BBC News

Published

on

Real Madrid

Real Madrid za ta karbi bakuncin Real Valladolid a wasan mako na hudu a gasar La Liga da za su fafata ranar Laraba a Alfredo Di Stefano.

A kakar bara Real ta hada maki hudu a kan Valladolid, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 ranar 24 ga watan Agustan 2019 a karawar farko.

A wasa na biyu a La Liga da suka fafata a gidan Valladolid, Real ce ta yi nasara da ci 1-0 ranar 26 ga Janairun 2020.

Kuma Nacho Fernandez ne ya ci wa Real kwallon saura minti 12 a tashi daga wasan.

A kakar bana Madrid ta yi canjaras a gidan Real Sociedad ranar 26 ga watan Satumba, kwana shida tsakani ta je ta doke Real Betis da ci 3-2.

Tuni dai kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana ‘yan wasa 22 da za su fuskanci Valladolid.

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin and Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal, Sergio Ramos, R. Varane, Nacho, Marcelo, Odriozola and F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Modrić, Casemiro, Valverde, Ødegaard and Isco.

Masu buga gaba: Benzema, Asensio, B. Mayoral, Lucas V., Jović, Vini Jr. and Rodrygo.

Wasu wasannin La Liga 10 da Real Madrid za ta buga nan gaba:

Lahadi 04 ga Oktoban 2020

Lahadi 18 ga Oktoban 2020

Lahadi 25 ga Oktobvan 2020

Lahadi 1 ga Nuwambar 2020

Lahadi 8 ga Nuwambar 2020

Lahadi 22 ga Nuwambar 2020

  • Villarreal da Real Madrid

Lahadi 29 ga Nuwambar 2020

Lahadi 6 ga Disambar 2020

Lahadi 13 ga Disambar 2020

  • Real Madrid da Atl Madrid

Lahadi 20 ga Disambar 2020

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending