Connect with us

Buhari

Najeriya ta yi hasashen bunƙasar tattalin arziƙi da kashi uku a kasafin 2021 | BBC Hausa

Published

on

@NigGov

Bayanan hoto,
Kimanin mako biyu ke nan da sanya dokar hana fita a wasu biranen Najeriya

Majalisar zartarwar Najeriya ta yi hasashen bunƙasar tattalin arziƙi da kashi uku cikin 100 da kuma hauhawar farashi da kashi 11.95 cikin 100 a kasafin kuɗin 2021.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito fadar shugaban ƙasar inda ta ce majalisar zartarwar tana hasashen ƙasar za ta rinƙa fitar da ko wace gangar man fetur kan dala 40, da kuma samar da gangar mai miliyan 1.86 a kowace rana a kasafin kuɗin.

Sakamakon irin illar da annobar korona ta yi wa Najeriya, tattalin arziƙin ƙasar ya ragu da kashi 6.1 cikin 100 a watanni shida na farko na 2020.

Wannan na nufin ƙasar za ta fuskanci matsin tattalin arziƙi a cikin watanni tara na farko na wannan shekarar, inda gwamnatin ƙasar ke hasashen cewa tattalin arziƙin ƙasar zai ƙara raguwa da kusan kashi 8.9 cikin 100.

Faɗuwar farashin man fetur a kasuwannin duniya ya sake yi wa ƙasar illa, ƙasar da ta dogara da man fetur.

Ƙasar ta yi kasafin kuɗin naira tiriliyan 13.08 a shekarar 2021 da kuma giɓin tiriliyan 4.48, inda aka saka dala kan farashin canji da ya kai 379 a kowace naira guda.

Kasafin dai sai majalisun tarayya sun duba shi da kuma yi masa kwasmwarima idan buƙatar hakan ta taso kafin a mayar wa shugaban ya sa hannu a kansa har ya zama doka.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending