Connect with us

Hausa

Zaɓen Amurka Na 2020: Abin da kuke buƙatar sani kan muhawarar Trump da Biden

Published

on

Biden da Trump

Mun sami muhimman bayanan abubuwan da aka tsara tattaunwa a muhawarar bayan shafe tsawon lokaci ana yakin neman zabe, wanda da alama ya kusa zuwa karshe.

A fagen muhawara a kan bar ‘yan takara ne da halinsu, sannan a dukkanin lokutan yakin neman zabe wannan ne lokaci mafi hadari a garesu.

Za a iya samun matsala sosai, don haka sukan yi taka-tsan-tsan.

Yaushe – kuma a ina – ne za a yi muhawara tsakanin Biden da Trump ?

Akwai muhawara uku ta shugaban kasa da aka tsara.

Ranar 29 Satumba a Cleveland, dake jihar Ohio.

Ranar 15 ga Oktoba a Miami, dake jihar Florida

Ranar 22 Oktoba a Nashville, dake jihar Tennessee

Mataimakin shugaban kasa Mike Pence da Sanata Kamala Harris suma za su fafata gaba da gaba:

Za a yi muhawarar ne a ranar 7 ga watan Oktoba a Salt Lake dake jihar Utah

Za a haska muhawarar tun daga farko har karshe a kafafen watsa labarai ba tare da saka wani talla ba

Menene tsarin tattaunawar farko?

Bayanan hoto,
Trump da Biden za su yi muhawara sau uku kafin zabe

Za a musu tambayoyi shida a bangaori daban daban har guda shida , kowanne bangare kuma za a kwashe mintuna sha biyar ana tattauna shi.

  • Gwagwamayar Trump da Biden
  • Batun kotun koli
  • Annobar korona
  • Rikicin kabilanci da tashin hankali a wasu jihohin kasar
  • Ingancin zaben
  • Tattalin arziki

Kowanne daga cikinsu zai samu minti biyu don amsa tambayar da za a yi masa kafin a fara mayarwa juna martani.

Me mutane za su sa ran gani a muhawarar ?.

Sharhi daga Anthony Zurcher, wakilinmu na kudancin Amurka

Donald Trump dai yana da kwarewar magana sosai, ya kan mamaye tattaunawa a cikin jma’a, kuma ƙarfinsa da raunin sa sananne ne ga yawancin Amurkawa.

Wannan shi ne dalilin da ya sa za a fi mayar da hankali kan irin rawar da Biden zai taka kawai.

Aikin Biden zai kasance ne kokarin bai wa mara da kunya, dole ne ya nuna wa Amurkawa cewa zai iya mulkarsu.

Sannan dole ne ya korewa jama’ a tunanin da Trump ya shuka a zukatansu, na cewa bashi da cikakkiyar lafiyar da zata bashi damar gudanar da al’amuran kasar yadda ya kamata.

Aikin Trump kuwa, zai kasance shi ne tunkarar abokin hamayyarsa. Kamar yadda Hillary Clinton da abokan hamayyarsa na farko za su iya tabbatarwa, ya kasance mai rikitarwa, mara tabbas kuma zai iya gwara kan yan Democrat sannan ya haifar musu da rikicin cikin gida da rashin yadda da juna.

Sai dai a lokaci guda kuma zai yi shirin mayar da martani a kan kalubalen da Biden zai rika yi masa, musamman kan salon gwamnatinsa na yaki da annobar korona da tattalin arziki da kuma sauran ayyukan shugaban kasa.

Mutumin da zai jagoranci muhawaar shine Chris Wallace, na kafar talabijin ta FOX.

Mutane da dama na ganin cewa dan jaridar na FOX zai saukakawa Trump, amma abin da ya kamata mutane su sani shi ne Wallace fa ba Sean Hannity bane.

Sun sha bam-ban kwarai da gaske.

A wata hira da suka yi da Trump a watan Yuli ya fada wa Trump kiri – kiri cewa ya sani shima fa an masa irin gwajin kwakwalwar da Trump ke ta kurarin an masa, kuma ya sani cewa gwajin ba wani kayan gabas bane.

Trump wanda ke shiri sosai da kafar talabijin ta FOX, ya sha sukar Wallace, wanda tsohon wakilin kafar talabijin ta CBS ne.

Wallace wanda ke da rijistar jam’iyyar Democrat ya ce jagorantar muhawara abu ne mai muhimmanci a gare shi, domin tana taimakawa miliyoyin ‘yan kasar wajen zaben wanda zai jagorance su.

A muhawara ta biyu kuwa mai gabatar da shiri na kafar talabijin ta C-Span Steve Scully ne zai yi jagoranci.

A karshe wakilin kafar talabijin ta NBC Kristen Welker zai karkare da muhawara ta uku.

Wakilin jaridar USA Today Susan Page ce zata jagoranci muhawarar da za a yi tsakanin ‘yan takarar mataimakin shugaban kasa tsakanin Kamala Harris da Mike Pence.

Ga masu jefa kuri’a da yawa muhawara nishaɗi ce da faɗakarwa, sannan takan taimaka musu wajen tantance tasirin dan takarar da suke son zaba.

Muhawara ta farko da aka nuna kai tsaye ta talabijin a shekara 1960 an yi ta ne tsakanin matashin Sanata na jam’iyyar Democrat Sanata John F Kennedy da mataimakin shugaban kasa mai ci Richard Nixon.

Tawagar Mista Kennedy ta tabbatar da cewa ya kayatar matuka la’akari da yadda ya rika kurawa kyamara ido ba tare da shakku ba, yayin da Nixon ya rika sharba gumi, ko da yake a lokacin yana kokarin murmurewa ne daga rashin lafiya.

Mafi akasarin wadanda suka kalli muhawarar ta talabijin na da ra’ayin cewa John Kennedy ne yafi taka rawa a muhawarar saboda yadda ya rika jawabi ba tare da wani kame kame ba, yayin da wadanda suka saurara ta rediyo ke ganin cewa Mista Nixon ne ya fi taka rawa.

Bayan muhawaar dai Mista Kennedy ya zakuda gaba a kuri’ar jin ra’ayin jama’a da ake gudanarwa kafin zabe, duk da cewa ba za mu iya baku tabbacin cewa hakan ta faru ne saboda kwarjinin da masu kallo ta talabijin suka gani tattare da shi ba.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Ronald Reagan ya kayar da Shugaba Jimmy Carter a muhawararsu ta 1980 ta hanyar yin gajerun maganganu masu jan hankali.

Mista Carter yayi kokarin ya haskaka manufofi da tarihi da sauran batutuwa da dama, yayin da shi kuma Reagan ya tafi a kan layi daya.

Sannan ya rika tsokanar Mista Carter a kan sukar da ya jima yana yi masa, in da da zarar ya soke shin sai yace “Ai kaji !”

A shekarar 2000, ana ganin jan numfashin da dan takarar Democrat Al Gore ya rika yi ne ya zamo silar rasa samun nasarassa a zaben da aka gudanar, domin ga kusan kowa ma, jan numfashi yayin da kake sauraron maganar wani na nuna alamun ka gamsu da ra’ayinsa ne.

A lokacin Geoge Bush na Republican ya bayyana wa Amurkawa kansa a matsayin mai tawali’u harma ya rika mu’amalantarsu sosai.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending