Connect with us

Hausa

An kama matar da ta aikawa shugaba Trump ambulan dauke da guba

Published

on

Masu bincike

‘Yan sanda a Amurka sun kama wata mata da ake zargi da aika wa shugaba Trump wata ambulan dauke da mummunar guba.

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce matar da yanzu haka ake tsare da ita a Buffalo na da katin shaidar zama ‘yar kasar Canada.

Rahotanni sun ce ranar Lahadi ne aka yi wannan kamu, yayin da take shirin shiga New York, wasu rahotannin kafafen watsa labaran cikin gida a kasar sun ce tana dauke da bindiga a lokacin da aka kama ta.

An kama Ambulan din ne makon da ya gabata a wani ofishin gwamnatin Amurka da ke tantance sakonni kafin aika su fadar White House.

Hadin gwiwar jami’an tsaron kasar masu yaki da ta’addanci a Washington na jagorantar bincike don gano ko tun yaushe ta aike da sakon.

Wannan shi ne karo na biyu da wani ya yi kokarin aika guba ta irin wannan hanya ga Mista Trump.

A shekarar 2018, hukumomin kasar sun kama wasu sakonnin da ake zargi dauke da sinadarin Ricin wanda aka aika wa shugaban.

Ma’aikatar Shari’ar Amurka ta ce wanda ake zargin, wani tsohon sojan ruwa ne mai suna William Clyde Allen,.

An gurfanar da shi a kotu a wannan lokaci kan tuhume-tuhume bakwai ciki har da amfani da guba a matsayin makami.

(BBC Hausa)

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending