Connect with us

Hausa

Biri ya ɗauki hoton selfie da wayar wani mutum da ta ɓata

Published

on

Monkey selfie

Bayanan hoto,
Wannan hoton selfie din wani biri ne daban da ya taɓa janyo badakala a kotu

Wani mutum dan kasar Malaysia ya ce ya ga hoton ‘selfie’ da bidiyo na wani biri a kan wayarsa da ta ɓata kwana guda bayan gano wayar a wani daji a bayan gidansa.

Hotunan da bidiyon sun nuna wani biri yana ƙoƙarin cinye wayar – kuma an yi ta yaɗa su a shafukan sada zumunta tun bayan da Zackrydz Rodzi ya wallafa a Twitter.

Ɗalibin ya ce da farko ya dauka an sace wayar ne a lokacin da yake bacci.

Sai dai har yanzu ba a gane asalin yadda wayar ta ɓata ba.

Haka kuma ba a iya gano yadda hotunan da bidiyon suka shiga wayar.

Bayanan hoto,
Hoton da Mista Zackrydz ya ce ya gani a wayarsa

Mista Zackrydz mai shekaru 20 ya shaida wa BBC cewa ya gane wayarsa ta bata ne bayan da ya tashi bacci kusan ƙarfe 11 na safiyar Asabar.

“Babu alamun fashi. Abin kawai da na yi tunani shi ne watakil tsafi ne,” kamar yadda dalibin mai karatun kimiyyar kamfuta a jihar Johor ya ce.

A wani bidiyo da aka aika wa BBC, an ga biri yana ƙoƙarin cinye wayar. Dabbar ta ƙura wa kyamarar wayar ido yayin da a bayansa ana iya ganin ganyayyaki da tsuntsaye.

Haka kuma, akwai wasu hotunan birin da bishiyoyi da tsirrai a kan wayar.

Bayanan hoto,
Wani hoton birin da Mista Zackrydz ya ce ya gani a wyarsa

Mista Zackrydz ya ce ya gaza gano wayar tasa har sai ranar Lahadi da rana, a lokacin da mahaifinsa ya lura da wani biri a wajen gidansa. Yana kiran wayar sai ya ji tana bugawa a wani daji daga bayan gidansu, a cewarsa, sai kuma ya gano wayar lulluɓe da taɓo a kan wasu ganyayyaki a ƙarƙashin bishiyar kwakwa.

Kawunsa ya yi masa ba’ar cewa watakil a samu hotunan barawon wayar a cikinta, don haka bayan da ya goge ta sai ya bude wurin hotuna inda a nan ne ya yi kicibis da hotunan birin.

Matashin ya ce ba a saba ganin birrai na rayuwa a kusa da gidaje ba, a unguwarsu birrai ba sa sata a gidajen mutane. Amma ya ce yana zargin birin ya shiga gidansu ne ta tagar ɗakin yayansa.

“Abin da bai wuce ka gan shi sau ɗaya cikin shekaru ɗari ba,” ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, kuma an yada sau da yawa sannan kafofin yaɗa labaru sun ta bibiyar labarin.

Bayanan hoto,
Wannan hoton selfie din wani biri ne daban da ya taɓa janyo badakala a kotu

Ba wannan ne karon farko da biri ya dauki hoton ‘selfie’ ba sannna ya yi kaurin suna. A shekarar 2017, wani mai ɗaukar hoto ɗan Burtaniya ya yi shari’a da wata ƙungiyar kare haƙƙin dabbobi bisa wani hoto da wani biri ya ɗauka.

A shekarar 2011, Naruto, wani biri a dajin Indonesia ya ɗauki abin ɗaukar hoton David Slater daga Monmouthshire kuma ya ɗauki hotunan “selfie” da ita.

Mista Slater ya dage a kan cewa shi ne mai hoton da akai ta yaɗawa a duniya, amma ƙungiyar kare haƙƙin dabbobi ta Peta ta ce ya kamata dabbar ce za ta ci gajiyar hoton saboda ita ta danna abin daukar hoton.

Wata kotu a Amurka ta yi watsi da ƙarar inda ta ce dabba ba za ta iya zama mai haƙƙin mnallakar hoton ba amma Mista Slater ya amince ya bayar da gudunmowar kashi 25 cikin 100 na duk wani kuɗi da zai samu nan gaba ga kungiyoyin agaji da ke kula da Naruto da sauran birrai irinsa a Indonesia.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending