Connect with us

Crime

NDLEA ta bankado kwantena makare da Tramadol a Legas – AREWA News

Published

on

Hukumar NDLEA dake hana sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta samu nasarar kama wata kwantena mai tsawon kafa 40 dake dauke da kwayar maganin Tramadol a tashar jirgin ruwa dake Lagos.

Bayanin haka na kunshe ne cikin wata sanarwa da John Achema mai magana da yawun hukumar ya fitar.

A cewar sanarwar, shugaban hukumar,Muhammad Abdallah ya ce kama kwantenar na zuwa ne bayan da a yan kwanaki jami’an yan sanda suka kama wata kwantenar dake makare da Tramadol da kuma wasu magunguna da aka haramta su shigowa da kuma yin amfani da su.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa, jami’an hukumar dake aiki a Apapa sune suka samu nasarar kama kwantenar dauke da kwayar magani da ake zargin Tramadol ne da kuma Codeine.

Abdullahi, ya ce binciken farko da suka yi ya nuna cewa akwai katan 255 na nau’ikan Tramadol iri-iri.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending