Connect with us

Education

Covid-19: Jihohin Najeriya da ɗalibai za su koma makarantu

Published

on

Nigerian schools resumption date

Jihohi da dama a Najeriya za su buɗe makarantunsu a watan Satumbar 2020 duk da cewa hukumomin tarayyar ƙasar sun bayar da shawarar a yi taka tsan-tsan.

Ministan Lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ya bayyana cewa har yanzu korona na kisa, haka kuma ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasar ta gargaɗi gwamnatin tarayya kan cewa kada a kuskura a buɗe jami’o’i a halin yanzu.

Sai dai akwai makarantun sakandire da firamare da jami’o’i da dama na jihohi da suka bayyana ranakun komawarsu domin soma sabon zagon karantu na 2020/2021.

Abuja – Birnin Tarayya

‘Yan ajin ƙarshe a sakandire sun koma tun 4 ga watan Agusta

Babu ranar da aka bayyana a birnin na komawa makaranta har sai gwamnatin tarayya ta bayar da cikakken izini.

Legas

‘Yan ajin ƙarshe a sakandire sun koma tun 4 ga watan Agusta

Makarantun firamare da sakandire za su buɗe 21 ga watan Satumba

Jami’o’in jihar kuma 14 ga watan Satumbar 2020.

‘Yan ajin ƙarshe a sakandire sun koma tun 4 ga watan Agusta

Har yanzu gwamnatin jihar ba ta bayyana ranar komawa makaranta ba.

Kwara

‘Yan ajin ƙarshe a sakandire sun koma tun 4 ga watan Agusta

Osun

‘Yan ajin ƙarshe a sakandire sun koma tun 4 ga watan Agusta

Makarantun firamare da sakandire za su koma tsakanin 21 ga watan Satumba zuwa 30 ga watan October domin kammala zangon karatu na uku na 2020.

Za a fara sabon zangon karatu na farko daga 9 ga watan Nuwamba zuwa 22 ga watan Janairun 2021.

Zangon karatu na biyu kuma zai fara 1 ga watan Fabrairu zuwa 9 ga watan Afrilun 2021.

Zangon karatu na uku kuma zai fara ne daga 26 ga watan Afrilu zuwa 23 ga watan Yulin 2021.

Jami’o’i a jihar kuma za su buɗe daga 21 ga watan Satumbar 2020.

Oyo

‘Yan ajin ƙarshe a sakandire sun koma tun 4 ga watan Agusta

Gwamnatin jihar ta soke zangon karatu na uku na makarantun firamare da sakandire. Za a yi amfani da zangon farko ne kawai da na biyu wurin tantance ɗaliban da suka yi ƙoƙari domin zuwa aji na gaba.

Za a fara sabon zangon karatu daga 21 ga watan Satumbar 2020 zuwa 30 ga watan Yulin 2021.

Zangon farko zai kasance daga 21 ga watan Satumba zuwa 21 ga watan Disambar 2020.

Sai kuma zangon karatu na biyu zai fara ne daga 11 ga watan Janairu zuwa 9 ga watan Afrilu.

Zangon karatu na uku kuma zai fara ne daga 3 ga watan Mayu zuwa 30 ga watan Yuli.

Jami’o’i a jihar kuma za su koma ne daga 21 ga watan Satumbar 2020.

Delta

Makarantun firamare a jihar Delta za su koma bayan gwamnatin jihar ta buƙaci ‘yan aji shida na firamare su koma a ranar Laraba, 16 ga watan Satumbar 2020.

Duka malaman firamare a jihar za su koma aiki daga ranar Litinin, 14 ga watan Satumbar 2020, kamar yadda shugaban ɓangaren ilimi a matakin farko na jihar Delta, Mista Patrick Ukah ya shaida.

Ɗalibai za su fara bitar karatu da zarar sun koma makaranta.

‘Yan aji uku na sakandire za su koma a ranar 8 ga watan Satumbar 2020.

Tuni dama ‘yan ajin ƙarshe na sakandire suka koma domin fara jarrabawar WAEC.

Akwai kuma yiwuwar jami’o’i a jihar za su koma daga 21 ga watan Satumba a jihar.

Ribas

‘Yan aji uku na sakandire tuni sun koma domin fara shirye-shiryen jarrabawa

‘Yan aji shida na sakandire sun koma domin fara rubuta WAEC.

Sai dai a jihar tuni aka fara karatu ta intanet da kuma amfani da gidajen rediyo da talabijin wurin koyar da ɗalibai.

‘Yan firamare da sakandire da jami’o’i za su koma a ranar 14 ga watan Satumba.

Kogi

Gwamnatin jihar Kogi da ke arewacin Najeriya ta sanar da ranar Litinin, 14 ga watan Satumba a matsayin ranar buɗe duka makarantun jihar, kamar yadda kwamishinan ilimi, da kimiyya da fasaha na jihar, Wemi Jones, ya bayyana.

Benue

‘Yan aji shida da uku na sakandire ne kawai suka koma a jihar sakamakon har yanzu gwamnatin jihar ba ta sanar da ranar buɗe makarantun jihar ba.

(BBC Hausa)

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending