Connect with us

Arewa

Wasiƙa daga Afrika: Me ya sa ake barazana ga ‘yan jarida a Najeriya?

Published

on

Former Nigerian minister Femi Fani-Kayode at the Calabar press conference in August 2020

Bayanan hoto,
Tsohon minista Femi Fani-Kayode ya yi ta cin mutuncin ɗan jaridar kamar wanda aka yi wa baki

Cikin jerin wasiƙun da muke samu daga ‘ƴan jarida daga Afirka, tsohon babban editan jaridar Daily Trust, Mannir Dan Ali ya duba ƙalubalen da ‘ƴan jarida ke fuskanta a yayin gudanar da ayyukansu.

A Najeriya har yanzu ana tambayar ko me ya sa jami’an gwamnati suke yi wa ‘ƴan jarida kallon yaransu.

Wannan ya biyo bayan ƙurar da ta tashi sakamakon cin mutuncin da tsohon minista a Najeriya, Femi Fani Kayode kuma ɗan jam’iyyar adawa ta PDP ya yi wa wani ɗan jarida.

Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda Femi Fani-Kayode ya fusata saboda wata tambayar da ɗan jarida, Eyo Charles ya yi masa yayin wata hira da ‘yan jarida.

Mr Fani-Kayode, wanda ba ya riƙe da wani muƙami a gwamnati ko Jam’iyyar PDP, ya fito bainar jama’a yana rangadin ayyukan gwamnoni a sassan jihohin Najeriya.

Duk rangadin da ya gudanar, yana kiran taron ƴan jarida domin yaba wa ayyukan.

A Calabar ne babban birnin Cross River, jiha ta uku da ya kai ziyara a watannin da suka gabata inda Mista Fani-Kayode ya nuna bacin ransa lokacin da Charles ya tambaye shi kan wanda ke ɗaukar nauyin rangadin da yake: “Ba ka faɗa muna wanda ke ɗaukar nauyin tafiye-tafiyen da kake ba…”

Maimakon ma ya bari ɗan jaridar ya idar da tambayarsa, kawia Fani-Kayode ya kira shi “wawa” tare da cewa ya yi kama da talaka da ke karɓar cin hanci, kamar yadda ake zargin ƴan jarida na karɓar na goro da ake kira “brown envelopes” a Ingilishi.

Ni mun taɓa samun saɓani da shi, lokacin da yake cikin majalisar ministoci tsohon shugaba Olusegun Obasanjo shekaru goma da suka gabata.

Ya wuce zagi, ya faru ne a fadar shugaban ƙasa da ake kira Aso Rock inda ya yi barazanar zai mare ni, sai da sauran ƴan jarida suka shiga tsakani.

Ban san dalilin da ya sa a lokacin ya fusata ba; sai daga baya na gano cewa ashe saboda wata hirar da ya yi da BBC game da kudirin Obasanjo na tazarce.

Hirar ta ja hankali kuma shi ne dalilin da ya sa ya nemi ya huce akaina a matsayin wakilin BBC a fadar shugaban ƙasa a lokacin.

Ba wai Mista Fani-Kayode ba ne kaɗai ke ɗaukar ƴan jarida a matsayin abin haushi ba.

A watannin baya, gwamnan jihar Ebonyi a kudu maso gabashin Najeriya ya kori wasu ƴan jarida guda biyu a yankin kan abin da ya kira yadda suke bayar da rahotannin da ba su dace ba game da jihar.

“Idan kana tunanin kana da alƙalami, mu muna da bulala,” kamar yadda gwamnan ya yi barazana ta hanyar amfani da wata kalmar salon magana ta linzamin doki.

Shekaru da dama a jaridar Daily Trust, dole muka janye wakili daga jiha bayan wasu zauna gari banza sun masa duka a wani taro bayan gwamna ya nuna ba so n rahotanninsa.

A cikin martaninta kan abin da ya faru kwanaki game da Fani-Kayode, Amnesty International ta yi allawadai da yadda aka walaƙanta ɗan jaridar.

Suka daga bangarori da dama, ya tilastawa Mista Fani-Kayode neman afuwa ga ɗan jaridar – ko da yake har yanzu yana yi wa Daily Trust barazanar cewa zai ɗauki matakin shari’a kan wani zane da jaridar ta yi game da batun.

A bayyane yake wannan ba shi ne na ƙarshe ba kan takun-saƙa tsakanin ƴan jarida da kuma manyan masu faɗa aji a Najeriya.

Wasu hukumomin gwamnati da manyan kamfanoni suna haramta ba kafafen yaɗa labarai tallace-tallace saboda ba su jin daɗin rahotannin da suke bayar wa.

Baya ga barazana da kuma furta munanan kalamai, akwai kuma wasu hanyoyi da kafofin yada labarai a Najeriya a ƙasashen Afirka suke tafiya a haka.

Saboda akwai ƙarancin albashi wani lokaci ma ba a biyan albashin a wasu kafafen yaɗa labarai, wanda hakan ke nufin wasu ƴan jaridar sun dogara ne da wanda zai biya su.

Wasu ma sukan buƙaci sai an biya su kuɗi kafin su ɗauki labari.

Fadar mabarata

Bisa ƙwarewa ta a matsayin ɗan jarida a Najeriya, ba wai masu hannu da shuni ba ko manyan masu faɗa aji ne suka ɗauki ƴan jarida a matsayin masu karbar na goro ba.

Wani babban misali shi ne wani shugaban mabarata a matattarar da ake zube shara a Ijora Badia a Legas.

Na tafi don na yi hira da shi a BBC a wajajen 1990 domin gano abin da ya yi kan yunƙurin hukumomi na janye mabarata daga saman titi zuwa wata cibiyar farfaɗo da su.

Yana wajen da ya kira fadarsa da aka gina can saman katakayyan shara.

Bayan haka, ya dage wai sai na karɓi kuɗi daga hannunsa.

Bayanan hoto,
Wasu ‘yan jarida suna son a rika ba su kudi idan suka halarci taro

Na ƙi karɓa har sai da na yi masa dogon bayani don ya fahimci cewa ba ni buƙatar na karɓi kudi daga wajensa don na gudanar da aiki na.

A kwana baya a ofishin jekadancin Amurka ranar bikin ƴancin faɗin albarkacin baki, wani ƙaramin dan jarida yake son sanin dalilin da ya sa babu kyau a karɓi kuɗi a yayin ɗaukar rahoto a wajen wani taro.

Yana ganin kamar biyan waɗanda suka yi jawabi ne a wurin taron.

Ɗaya daga cikin masu jawabi a wurin taron ya yi masa bayani ta hanyar amfani da karin magana cewa “hannun bai bayarwa a kullum yana saman hannun mai karɓa” – wato yana nufin idan ɗan jarida yana karɓar irin waɗannan kyaututtukan, to shi ko ita yana da wahala su iya yin adalci ko kuma yin tambaya mai tsauri.

Abin baƙin ciki a Najeriya a irin wannan yanayin da ba a irin waɗannan tambayoyin, ɗan jarida na iya samun kansa a irin abin da Fani-Kayode ya aikata.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending