Connect with us

Arewa

Boko Haram: An yi kashe-kashe tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan ISWAP a jihar Borno

Published

on

mayakan Boko Haram

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa an samu ƙarin tashe-tashen hankali tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan ƙungiyar ISWAP wadda ta balle daga ƙungiyar Boko Haram.

Ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya ta ISWAP ta ce mayaƙanta sun kashe sojojin Najeriya aƙalla 20 a hare-hare biyu da suka kai kan sojojin a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Rahotanni na cewa masu tayar da ƙayar bayan cikin motoci da aka girke manyan bindigogi a kansu, sun kai hari ne a wani sansanin soji da ke Magumeri, kimanin kilomita hamsin daga Maiduguri babban birnin Jihar ta Borno.

Me ISWAP ta ce?

Cikin wata sanarwa, kungiyar ISWAP wadda ta ɓalle daga Boko Haram, ta yi ikirarin cewa mayakanta sun kashe sojoji goma da kuma kwace makamai da motocin soji a yayin arangama da suka yi.

Kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa ta kashe wasu karin sojoji 10 a wani kwanton-bauna kan ayarin sojojin a kusa da kauyen Kuros-Kauwa da ke yankin Baga.

Duka lamuran biyu sun faru ne a ranar Talata. Kawo yanzu babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin masu tayar da kayar bayan.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa majiyoyinsa sun tabbatar masa da cewa sojoji tara mayakan suka kashe a Magumeri.

Me rundunar sojin Najeriya ta ce?

Rundunar sojin Najeriya ba ta ce uffan ba kan lamarin, kuma duk kokarin da BBC ta yi na jin ta bakinta ya ci tura domin kakakin hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo-Janar John Enenche, bai amsa kiraye-kiraye ta wayar tarho ba.

To sai dai a wata sanarwa, rundunar sojin ta yi ikirarin kashe mayakan kungiyar ta ISWAP a wani farmaki ta sama da dakarunta suka kai da jiragen yaki kan matsugunan masu tayar da kayar bayan a kauyen Kaza, kusa da Gulumba-Gana a yankin Bama cikin jihar ta Borno.

Shi ma farmakin, a ranar Talata sojojin suka kai, wato ranar da kungiyar ta ISWAP ta yi ikirarin kashe sojojin.

A watan Agustan da ya gabata ma sai da Ƙungiyar IS ta ce ta kashe sojojin Najeriya guda bakwai a garin Kukawa da ke jihar Borno a arewacin Najeriya, yayin da rahotanni suka ce kuma mayakan sun kuma yi garkuwa da mutane da dama a garin.

A baya-bayan nan dai sojojin Najeriya na kara ƙaimi a hare-hare ta sama da suke kai wa kan masu tayar da kayar baya a yankin Tafkin Chadi.

Ayyukan tayar da kayar baya na kungiyar Boko Haram da kuma ISWAP da ta ɓalle daga cikinta, sun yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 30,000 da kuma raba miliyoyi da muhallansu a ƙasashen Najeriya, da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending