Connect with us

Hausa

Kasar Ghana: Yadda tsohuwa ta rasa ranta saboda zargin maita

Published

on

Rahotanni daga Ghana sun ce jama’a na ci gaba da nuna bacin ransu kan kisan wata tsohuwa mai shekaru 90 da wani gungun mutane suka yi bisa zargin ta da maita.

A cewar rahotannin, an kashe matar ne bayan da wani boka ya ce ita mayya ce abin da ya sa mutanen suka yi mata duka har ta mutu yayin da wasu ke kallo.

Lamarin dai ya faru ne a garin Salaga da ke lardin Savanah a arewacin kasar.

Abdulwahab Jawando, wani ɗan jarida a Ghana, ya shaida wa BBC cewa wani boka mai suna Tanko shi ne ya yi zargin Madam Akua Denteh da haifar da rashin ruwan sama na tsawon watanni a unguwar.

A cewarsa, ba wannan ne karon farko ba da ake zargin wasu da hannu a rashin samun ruwan sama a yankin.

Ya ce “wannan zargi an fi yi wa mata kuma tsofaffi kuma talakawa shi.”

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending