Connect with us

Arewa

Lazarus Chakwera: Shugaban kasar Malawi ‘da ke jayayya da Ubangiji’

Published

on

Lazarus Chakwera addressing a campaign rally (file pic)
Hakkin mallakar hoto
Reuters
Image caption

Lazarus Chakwera

A wani salo irin na masu wa’azi, sabon shugaban Malawi, Lazarus Chakwera ya nemi hadin-kai ‘yan kasar jim kadan da rantsar da shi a ranar Lahadi.

Wannan makon ya kasance bambarakwai bayan tsohon shugaban cocin Malawi Assemblies of God, daya daga cikin manyan cocin kasar, ya hau mumbari yana amfani da kalmomin da ke kama da na wa’azi wajen yi wa al’umma jawabai.

Akwai rabuwar kawuna a kasar bayan shafe tsawo wata 13 ana rikici kan zaben 2019 da kotu ta soke.

A lokacin da yake jawabi cikin salo irin wanda aka saba ji daga jagoran masu fafutuka na Amurka Martin Luther King, Shugaba Chakwera ya yi magana a kan buri ”da hadin-kai wajen cimma bukatun rayuwa da samun wanzuwa, inda yake cewa ba wai batun ‘yanci kawai za a ke yi ba”.

Lazarus Chakwera

Jacob Nankhonya

We all must wake up because this is a time to arise from slumber and make our dream come true”

Sai dai ya ce ba abu ne mai kyau ba mutum ya zama kawai buri gare shi.

”Lokaci ya zo da ya kamata tunaninmu su zarce na buri.

”Dukkanin mu sai mun tashi tsaye saboda yanzu ne lokacin da zamu farka daga baccin da muke yi don ganin burikanmu sun cika.”

Mista Chakwera mutumin Allah ne mai zurfin addini.

Sabon shugaban mai shekara 65 a duniya, ya yi nasarar zama shugaban Jam’iyyar Malawi Congress a 2013 ba tare da wani ilimi ko sani mai zurfi kan harkokin siyasa ba.

Jayayya da Ubangiji

Ya soma wannan aikin ne bayan shugabantar Cocin Assemblies of God na tsawon shekaru 24, sai dai a lokacin da ya fito takarar shugabancin kasar a 2014 ya ce, yanke shawarar shiga siyasa ba abu ne mai sauki ba.

”Na sha musu da Ubangiji kan alkibilar rayuwa da dama, wanda a wurina nake jin ba daidai ba ne,” kamar yadda ya fada a wani bidiyo da Cocin St Andrew’s Presbyterian ya wallafa a California.

Sai dai bayan tattaunawa sosai ”Ubangiji yana mai cewa: Na fadada nauyin da ke kanka saboda ka zama limami ga kasa baki daya”.

A wata hira, a shekarar 2017, ya ce a tattaunawar da ya yi da Ubangaji ya bude shafi na Uku na littafin Bible, a lokacin da Ubangiji ya bayyana ga Musa sannan ya umarci shi ya jagoranci fitar Israelites daga Masar

Wannan ya nuna yadda shugaba zai iya shawo kan batun da ya shafi addini da kuma bukatun yau da kullum na mutane, a cewar mataimakinsa Sean Kamponden a tattaunawarsu da BBC.

Sai dai bashi da niyya ko fatan mayar da Malawi wata kasa da ke bin addini ko ba ya so ya zama mai wa’azi, a cewarsa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Image caption

An yi zanga-zanga kan zaben 2019 da kotu ta soke

”Shugaban ya ce ya yi amannar cewa gwamnati abu ne da Ubangiji yake samarwa a kasa, domin kawo ci gaban al’umma, da kuma wanzuwa,” a cewar Mista Kampondeni.

”A Malawi, yana ganin cewa tsarin tafiyar da cibiyoyin gwamnati sun durkushe sama da shekaru 25, akwai gazawa wajen samar da abubuwan bukatu don haka shi yanzu yazo ne domin bada gudunmawar cike gibin da aka haifar.”

Lazarus Chakwera

AFP

Lazarus Chakwera

President of Malawi

  • Born 5 April 1955
  • Studied theology in Malawi, South Africa and USA
  • Pastor and leader ofthe Malawi Assemblies of God church
  • Authored several books on religion including Reach the Nations
  • Ran for president in 2014 and came second
  • Became presidentin 2020 after defeating the incumbent

Source: BBC Monitoring

Tsaye cike da shaukin mulki lokacin da ya ke jawabi ga ‘yan kasar ranar Lahadi, Mista Chakwera ya taso ne a wani kauye da ke wajen birnin, Lilongwe, kuma kamar yadda ya saba shaidawa shi mutum ne mai kunya a lokacin yarintarsa.

Mahaifinsa Limamin coci ne wanda ya yi da’awa sosai da kafa coci-coci da dama, don haka ba abun mamaki ba ne idan ya yi gado daga wurin Ubansa.

Sai dai lokacin da ya ke sakandare, ya koyi turanci irin na turawan Amurka lokacin da ya ke kwaikwayon harshen malaminsa, burinsa kafin wannan lokaci shi ne ya zama likita.

Ya yi tunanin cewa idan ya girma a matsayinsa na likita, babu shi babu bayyana gaban cuncurundo mutane yana jawabai, kamar yadda ya shaida wa dan jarida Joad Chakhaza a shekara ta 2017.

Siyasa ko limanci

Amma ya ce a lokacin da yake makaranta ”’na tattauna da Ubangaji” sai ya soma sauya mun alkibilar rayuwata zuwa limanci.”

Yanzu dai mahaifi ga yara hudu na son amfani da wannan kuzarin da manufofinsa wajen mulkar kasar.

Ga wadanda ke ganin akwai bambanci sosai kan shugabanci irin na addini da siyasa, mashawarci ga Mista Chakwera ya ce shugaban yana da sani sosai kan harkokin siyasa.

”Duk wanda ya fahimci tsarin siyasarsa da gwagwarmayar da ta kai shi ga wannan mukami – zai fahimci siyasa ba wai shiga ofis ba ne kawai,” a cewar Mista Kampondeni.

”Kana bukatar shiga siyasa sosai kafin ka iya ma samun wani mukamin gwamnati.”

Sai dai, ya ce, tsari ko takun shugaban zai kasance na daban ba kamar wanda aka saba gani irin ta kazamar siyasa ba.

Yanzu ya zame masa dole ya yi amfani da kwarewarsa wajen hada kan kasar.

Hakkin mallakar hoto
AFP
Image caption

Mr. Chakwera

A jawabansa ga kasar ba wai kawai ga dandazon magoya baya da ke murnar nasararsa ba a Lilongwe, Mista Chakwera ya ce wadanda ba su jefa masa kuri’a ba watakila sun yi tunanin shugaban shi sa zai kasance na ”tsoro da jimami”.

Sai dai ya yi kokarin ba su gwarin gwiwa.

”Wannan sabuwar Malawin kasa ce ga kowa har tsawon lokacin da zan kasance kan wanan kujera, za ta kasance gidan da kowa zai samu habaka.”

Shugaban dai ya kada Peter Mutharika da kashi 59 cikin 100 na kuri’u, wannan watakil ya gamsar da mutane da ke da shakku a kansa a cewar dan jarida Chakhaza a tattaunawarsa da BBC.

Nuna kabilanci

”Akwai jan aiki a gabansa ganin cewa gwamnatin da ta gabata ta sha nuna kabilanci waje nade-nade, musamman daga yankunan tsakiya da arewacin kasar, a cewarsa.

Za a fuskanci matsi daga masu ganin cewa an daidata kasar kuma mutane za su nuna matsuwa na ganin an kawar da nuna bambanci.”

Magoya bayan shugaban na da yakinin zai kawo sauyi a shugabanci irin na tsoron Ubangiji da cika muradun ‘yan kasar.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending