Connect with us

Hausa

Adadin Masu Coronavirus Ya Zarta 25,000 a Najeriya

Published

on

Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta ce sabbin mutum 566 ne cutar COVID-19 ta harba cikin yini guda.

Hakan na nun adadin wadanda cuter ta harba a kasar ya kai 25,133 kamar yada hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter a daren jiya Litinin.

Cikin adadin jihar Legas ta samu mutum 166 da suka kamu da cutar.

Sauran jihohin sun hada Oyo 66, Delta(53), Ebonyi 43, Plateau 34, Ondo 32, Birnin tarayya Abuja 26, Edo 24, Ogun 25, Imo 15, Bayelsa 13, Benue12, Gombe 11, Kano 11, Kaduna11, Osun 8, Nasarawa 7, Borno 5, Katsina 2, Anambra 2.

A cewar hukumar, a yanzu haka Najeriya na da mutum 9,402 da suka samu lafiya, sai kuma mutum 573 da suka mutu.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending