Connect with us

Hausa

Liverpool: ‘Yan Afirka da suka taimaka mata lashe Premier League | BBC Hausa

Published

on

Salah and Mane

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Salah da Mane sun kasance cikin manyan ‘yan wasan da suka fi murza leda a a tarihin Premier League

Liverpool ta lashe gasar Firimiya – karon farko tun shekarar 1990. ‘Yan wasan Afrika da dama sun taka rawa wurin samun wannan nasara.

Ga irin rawar da suka taka:

Mo Salah

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwallon da Salah ya zura a wasansu da Manchester City ta kasance ginshikin lashe Kofin Firimiya da Liverpool ta yi

Dan kasar Masar ya kasance dan wasan da ke da magoya baya sosai a Anfield tun da ya soma buga mata wasa a 2017. Ganin cewa bai taka rawar gani ba a Chelsea a wasannin Premier, an yi tsammanin ba zai taka rawa irin wacce ya taka a Arsenal ba.

A kakar wasansa ta farko, ya zura kwallo 32 a wasanni 36 na gasar Premier. Sun kammala gasar a matsayi na hudu amma sun kai wasan karshe a gasar Zakarun Turai da suka fafata da Real Madrid – sai dai Salah ya ji rauni bayan Sergio Ramos ya bangaje shi.

Ta bayyana karara cewa idan Liverpool za ta kawo karshen jiran da ta kwashe shekara 30 tana yi don lashe gasar Firimiya, dole Salah ya taka rawa – kuma ya taka muhimmiyar rawa.

Salah shi ne dan wasan na biyu da ya fi zura kwallo inda ya ci kwallaye 17, kuma ya zura kwallo ta biyu mai muhimmanci a wasan da suka doke Manchester City da ci 3-1 a watan Nuwamba.

Kashin da Liverpool ta sha a hannun City a kakar wasan da ta wuce ne ya hana ta daukar Kofin Firimiya. A wannan karon, kwallon da Salah ya ci ce ta sanya Liverpool a matsayin da zai yi wahala ta koma baya.

Kazalika Salah ya ci kwallon farko a wasan da suke doke West Ham da ci 2-0 a watan Janairu – nasarar da ke nufin, a karon farko a tarihinta, Liverpool ta doke kowacce babbar kungiyar da ke buga gasar Firimiya a kakar wasa.

Sadio Mane

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mane ya ci gaba daga inda ya tsaya kafin annobar korona, inda ya zura kwallo a wasan da suka doke Crystal Palace da ci 4-0

Rawar da Salah ya taka a kakar wasansa ta farko a Anfield kenan. Shi ma abokin wasansa dan kasar Senegal ya taka muhimmiyar rawa.

A kakar wasa biyu da suka wuce, Mane ya nuna cewa shi ma ba kanwar lasa ba ne.

Mane ne ya zura kwallo ta uku a wasan da suka doke Manchester City – a wancan lokacin, ita ce kwallo ta 16 da ya zura a Anfield a shekarar 2019.

Amma a wasan da ya yi gabanin wancan, inda suka fafata da Aston Villa ranar 2 ga watan Nuwamba, Mane ya fi taka rawa.

Baya an ci su 1-0 minti biyar kafin a tashi wasa kuma wanda zai zama karon farko da suka sha kashi, Mane ya buga kwallon da Andy Robertson ya yi amfani da kansa wajen zura ta a raga inda suka tashi da ci 1-1.

Hakan ya kara wa Liverpool kwarin gwiwa kuma Mane ya sake samun kwallo inda a minti na 94 ya zura ta.

Naby Keita

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Keita ya taimaka sosai wajen zura kwallaye musamman a lokutan da Liverpool take tsaka mai wuya

Kwallo daya kacal dan wasan tsakiya na Guinea ya zura wa Liverpool a kakar wasa ta bana, a fafatawar da suka doke Bournemouth da ci 3-0, kuma galibi ya fi taka rawa ta shugaban tawaga a kakar 2019/20.

Amma ya taka muhimmiyar rawa wajen zura kwallo abin da ya kai kungiyar ga samun nasara a kakar wasan ta bana.

A watan Disamba, Liverpool ta je buga gasar Club World Cup a kasar Qatar – inda suka raba tawagarsu gida biyu ta yadda za su kuma samu damar buga gasar da ake yi a gida.

Jurgen Klopp yana so ya yi amfani da wasu ‘yan wasa a Qatar ba tare da ya sanya ‘yan wasan tawagar farko ba, a yayin da kuma yake son lashe Kofin Club World Cup. Don haka ya sanya Keita a bangarensa – kuma dan wasan ya taka muhimmiyar rawa.

Ya zura kwallo a ragar Monterrey a wasan dab da na karshe kuma ya buga wasan minti 100 a yayin da suke fafatawa da Flamengo, inda sai a hutun karin lokaci aka cire shi.

Joel Matip

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matip ya soma kakar wasan bana a tawagar farko, ko da yake an koma da shi benchi a yayin da Gomez ya murmure

Dan wasan na Kamaru ya taka rawa sosai a Liverpool – ya yi kokari sosai wajen tsayawa a tsakiya tare da Virgil van Dyke da matashin dan wasa Joe Gomez.

Rawar da Matip yake takawa ta takaita saboda gogayyar da Dejan Lovren yake yi da shi – amma duk da haka sau tara yana buga wa Liverpool wasa, kuma shi ne ya ci kwallon farko a wasan da suka doke Arsenal da ci 3-1.

Divock Origi

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Da alama Origi yana so ya buga wasa a fafatawa da Everton

Tabbas Origi yana buga kwallo ne a Belgium – sai dai mahaifinsa Mike dan kasar Kenya ne don haka muka saka shi a wannan jeri na ‘yan Afirka.

Origi ya sanya hannu kan kwantaragin tsawon lokaci da Liverpool ne ana dab da soma kakar wasan bana. An fi sanya shi domin maye gurbin wani dan wasan, sai dai duk da haka ya yi rawar gani wajen zura kwallaye – cikinsu har da kwallo biyu da ya ci a wasansu da Everton a wasan hamayya na Merseyside inda Liverpool ta ci 5-2.

Trending