Connect with us

Arewa

Ko Kun San Cewa Kudin Tallafin CBN COVID-19 Ba Kyauta Ba Ne, Bashi Ne? – AREWA News

Published

on

Idan ka cika kuma har ka samu kudin tallafin, to ina taya ka murna, amma fa ka sani ba kyauta ba ce, za ka biya.

Dole za ka biya ba tare da ma an turo maka jami’in tsaro ba. Dama idan aka baka tallafin za ka saka hannu ne akan cewar idan ba ka biya kudin ba, banki ta ciri kudinta duk lokacin da kudi ya shiga asusun bankin ka, ko naka ne ko ba naka bane.

Saboda haka ka yi amfani da kudin ta yadda ya dace domin ba kyauta ba ce, ba shi ne.

Ina kara tuna maka, matukar ka ki biyan kudin, bankin NIRSAL da CBN za su cire kudaden su a asusun ka koda kuwa kudin albashinka ne.

Haka kuma ka sani abinda za ka ga ka ya shigo asusun ka bashi ne ainihin abinda za ka biya ba. Ka sani akwai kashi hudu cikin dari na ruwa a ciki wato interest (4% interest) da kuma kudin gudanarwa.

A misali, idan kaga N425,100 sun shigo asusun ka, to ka sani abinda za ka biya shine N450,000 saboda kudin gudanarwa da ruwa.

Haka kuma abinda ake nufi da Moratorium shine tsawon lokacin da z ‘a ba mutum kafin ya fara biyan bashin shi kuma Repayment Period shine watannin da za a biya bashin a ciki.

Misali; idan za ka biya a shekara daya ne, za’a raba kudin da zaka biya dinne cikin watanni goma sha biyu (N450,000÷12 = N37,500). Kenan duk wata zaka biya N37,500 harna tsawon watannin goma sha biyu na shekara

Anan kaga ba wai ana nufin tunda kaga N425,000 misali, kace ai N425,000 ÷ 12) dole ya zama harda kudin gudanarwa da kudin ruwa na kashi hudu cikin dari.

Haka kuma har yanzu ina kara tuna muku cewar duk fa wadanda ya karbi kudin dole ne fa zai biya ba zaka taba tsallakewa ba koda kuwa ka mutu ne.

Kuma koda ka yi tunanin canza asusun banki ko canza suna dole banki ta yadda za ta nemo ka domin daga cikin abinda ba zaka iya canzawa ba akwai yatsar hannunka.

Haka kuma za su iya nemo wanda ya tsaya maka ya cigaba da biyan kudaden daga inda ka tsaya kafin ka mutu.

Haka kuma idan mutuwar ta zo ne bagatatan, shi wanda ya tsaya maka za a dan iya daga masa kafa na wani dan lokaci kafin ya fara biyan bashin.

Saboda haka ina kira gare ku da ku yi amfani da kudin wajen bunkasa sana’oin ku ko gonakinku.

Idan kuka yi haka da kyakykyawar zuciya, Allah zai sa kudin su cigaba da karuwa a samu riba a biya bashin.

Ina yi wa kowa fatar Allah yasa ya biya da hannunsa ba tare da wata matsala ba.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending