Connect with us

Hausa

Zlatan Ibrahimovic: Dan wasan AC Milan ya ji rauni a ƙafarsa

Published

on

AC Milan striker Zlatan Ibrahimovic

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ibrahimovic ya zura kwallo hudu a wasa 10 da ya buga wa AC Milan

AC Milan ta ce dan wasanta Zlatan Ibrahimovic ya ji rauni a ƙafarsa lokacin da yake atisaye ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa raunin da dan wasan mai shekara 39 dan kasar Sweden ya ji zai iya barazana ga sana’arsa ta kwallon kafa amma Milan ta shaida wa BBC Sport cewa za a yi masa gwaji ranar Talata.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce “Za mu san girman matsalar a lokacin.”

Tsohon dan wasan na Manchester United Ibrahimovic ya koma Milan a watan Disamba a yarjejeniyar wata shida kuma ya zura kwallo hudu a wasa 10 da ya buga wa kungiyar.

Abangare guda, gwamnatin Italiya za ta yanke shawara ranar Alhamis kan ranar da za a ci gaba da gasar Serie A.

An bai wa kungiyoyi damar komawa atisaye ranar 19 ga watan Mayu, kuma sun kada kuri’ar amincewa a koma gasar Serie A ranar 13 ga watan Yuni.

Hukumar kula da kwallon kafar Italiya ta kebe ranar 20 ga watan Agusta domin a kammala gasar sanna a soma kakar wasa mai zuwa ranar 1 ga watan Satumba.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending