Connect with us

Hausa

Ozil ba zai bar Arsenal a kakar wasan bana ba, RB Leipzig tana zawarcin Todibo

Published

on

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil, mai shekara 31, ba zai bar kungiyar a bazara ba inda ya ce zai ci gaba da yin bakin kokarinsa har karshen kwangilarsa.(Fanatik, via Football London)

Arsenal tana fatan ci gaba da rike dan wasan da ta karbo aro daga Real Madrid Dani Ceballos, mai shekara 23, har sai an kammala kakar gasar Premier ta bana, amma ba ta shirin tsawita zamansa zuwa kakar wasa mai zuwa. (El Confidencial, via Metro)

RB Leipzig ta bi sahun Everton a fafutukar ganin sun dauko dan wasan Faransa mai shekara 20 Jean-Clair Todibo daga Barcelona. (HITC)

Manchester United na son dauko dan wasan Argentina mai shekara 19, Thiago Almada, wanda ake rade radin zai koma Arsenal, dagaVelez Sarsfield. (Tutto Mercato Web, via Express)

Har yanzu Manchester United bata yanke hukunci game da sabunta kwangilar dan wasanta na tsakiya mai shekara 19 Angel Gomes ba, wanda kwangilrsa za ta kare a karshen watan Yuni. (Goal)

  • Aubameyang zai buga wa Madrid, Arsenal ta fuskanci matsala kan Upamekano
  • Za a ci gaba da gasar La Liga cikin watan Yuni

Manchester United tana zawarcin dan wasan Benfica Carlos Vinicius, a yayin da ake shirin sayar da dan kwallon na Brazil mai shekara 25 a kan £88m. (Sun)

Dan wasan Algeria Riyad Mahrez, mai shekara 29, ya ce Liverpool ta so sayo shi kafin Manchester City ta dauko shi daga Leicester City amma Liverpool ta janye bayan ta dauko Mohamed Salah daga Roma. (Bein Sports, via Manchester Evening News)

Chelsea tana da kwarin gwiwar dauko matashin dan wasa Charlie Webster, wanda rahotanni suka ce zai koma Borussia Dortmund, inda za ta ba shi kwangilar kwararrun ‘yan wasa idan ya kai shekara 17 a watan Janairu. (Telegraph)

Trending