Connect with us

Hausa

Coronavirus: Wanne rukunin mutane ne ya fi hatsarin kamuwa da cutar? | BBC Hausa

Published

on

tsofaffi

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tsofaffin mutane wadanda garkuwar jikinsu ba ta da kwari sun fi yiwuwar shiga matsala sosai idan suka kamu da coronavirus

Coronavirus za ta iya shafar kowanne mutum, amma mutanen da ke fama da wasu rashin lafiyar da kuma tsofaffi sun fi yiwuwar kamuwa da cutar.

Idan ka dade kana fama da rashin lafiya, za ka iya damuwa da jin wannan labari. Sai dai kwararru a fannin lafiya sun bayar da shawarwari.

Su wane ne ke fuskatar hatsarin kamuwa da cutar?

Ko da mutum yana fama da wasu cutukan, bai kai mutumin da ya yi mu’amala da wanda ke da cutar coronavirus yiwuwar daukar cutar ba.

Amma dai alamu sun nuna cewa tsofaffin mutane, wadanda garkuwar jikinsu ba ta da kwari da kuma mutanen da ke fama da wasu cutukan, irin su ciwon zuciya da ciwon suga da tarin fuka, sun fi yiwuwar shiga matsala sosai idan suka kamu da coronavirus.

Galibin mutane suna warkewa daga coronavirus cikin gaggawa idan suka samu hutun kwanaki kadan. Amma cutar takan zama barazana ga wasu, wasu lokutan ma takan zama ajalin masu dauke da ita.

Alalomin cutar sun yi daidai da na sauran cutuka gama-gari, irin su zazzabi da mura:

 • tari
 • zazzabi mai zafi
 • yankewar numfashi

Mutanen da ke da kasadar kamuwa da cutar su ne wadanda shekarunsu suka zarta 70, ko suna fama da wasu matsalolin rashin lafiya ko ba sa yi, da kuma mutanen da ke kasa da shekara 70 idan suna fama da wasu daga cikin wadannan cututtuka:

 • Matsanantan cutukan numfashi, irin su asthma, tsananin zafin kirji, yankewar numfashi da kuma matsananciyar mura
 • Matsanancin ciwon zuciya, da ya hada da daina aikin zuciya
 • Matsanancin ciwon koda
 • Matsanancin ciwon hanta
 • Tsananin ciwon kwakwalwa
 • Ciwon suga
 • Cutukan da suka shafi hanji – misali, ciwon sikila ko kuma idan an yi wa mutum tiyatar cire hanji
 • Cutukan da ke haddasa raunin garkuwar jiki, irin su HIV da AIDS, ko kuma kona kwayoyin cutar daji
 • Masu fama da teba
 • Mata masu ciki.

Ana bai wa mutane shawara su rika daukar matakan bayar da tazara wajen mu’amala da juna da zummar rage kasadar kamuwa da kuma yada kwayar cutar coronavirus.

An bai wa mutanen da ke da matukar hatsarin kamuwa da cutar shawara su bi wannan tsari sau da kafa.

Ina fama da asthma, me ya kamata na yi?

Hukumar Lafiya ta Burtaniya ta shawarci mutanen da ke fama da asthma su rika amfani da abin da ke taimakawa wajen yin numfashi ko inhaler, a Turance kullum kamar yadda aka saba.

Hakan zai taimaka wajen hana fuskantar yiwuwar katsewar numfashi, wanda kwayar cuta irin coronavirus ke haddasawa.

Ya kamata mutum ya rika ajiye inhaler dinsa a kusa da shi kowacce rana, ko da zai ji alamun tashin asthma.

Idan asthma ta ta’azzara kuma ka ga cewa ka fada hatsarin kamuwa da coronavirus, ka tuntubi hukumomin lafiya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Na manyanta, shin ya kamata na killace kaina?

Shawarar da babban likitan gwamnati ya bayar ga kowa – ba tare da matsayin shekarunsa ba – ita ce ya daina musabaha ko matsawa kurkusa da wasu mutanen domin kauce wa kamuwa da coronavirus.

Hakan na nufin mutum ya guji shiga tarukan jama’a.

Hakan na da matukar muhimmanci musamman ga tsofaffin da suka wuce shekara 70 da kuma mutanen da ke fama da wasu cutukan saboda suna cikin kasadar kamuwa da cutar.

Me zan yi idan ina fama da matsanaciyar rashin lafiya?

Duk mutumin da ke cikin matukar kasadar kamuwa da kwayoyin cuta irin su mura da zazzabi ya kamata ya dauki matakan kare kansa daga cutukan.

Mutane da suka nuna alamun kamuwa da cutar – wadanda suka soma tari ko mura – ya kamata ya zauna a gida. Idan alamomin cutar suka fito fili sosai kuma mutum bai samu sauki ba tsawon kwana bakwai, ya kamata ya tuntubi likita.

Ina da ciwon suga, me ya kamata na yi?

Mutanen da ke fama da nau’i na 1 da na 2 na ciwon suga suna da matukar kasadar kamuwa da coronavirus.

Dan Howarth, shugaban cibiyar kula da masu ciwon suga ta Burtaniya, ya ce : “Coronavirus ko Covid-19 tana iya ta’azzara ciwon suga.

“Idan kana da ciwon suga kuma ka ga alamomi irin su tari da zazzabi mai zafi da yankewar numfashi, akwai bukatar ka duba yanayin hawa da saukar suganka akai-akai.”

Idan ka ga irin wadannan alamomi ya kamata ka zauna a gida tsawon kwana bakwai, sannan ka ci gaba da shan magungunanka. Kada ka je asibiti ko wurin likita, ko da kuwa ka shirya ganin likita.

Idan ba ka ga wata alama ta kamuwa da coronavirus ba kuma kana son ganawa da likitanka, ya kamata ka tuntube shi ta hanyar intanet ko wayar tarho maimakon ziyartarsa ido da ido.

Shin ya kamata mata masu ciki su damu?

Babu wata shaida da ke nuna cewa matan da ke da ciki (da jariransu) na fuskantar hatsarin kamuwa da coronavirus, amma gwamnati ta yi kira a gare su, su kara kula da lafiyar kansu.

Kamar kowa, ya kamata su dauki matakan kariya domin gudun kamuwa da cutar. Suna cikin jerin mutanen da ake so su rage musabaha ko taba mutane, kamar yadda jami’an lafiya suka bayar da shawara.

Jami’an lafiyar mata sun bayar da shawarwari kamar haka:

 • Idan kina dauke da cikin da bai wuce mako 28 ba kuma ba kya fama da wata rashin lafiya ta daban, ya kamata ki yi nesa-nesa da jama’a amma dai za ki iya ci gaba da aiki, sai dai akwai bukatar kada ki yi jinyar mutanen da ke fama da coronavirus, har sai idan za ki yi amfani da kayan kariya.
 • Idan kina da cikin da ya wuce mako 28 ko kuma kina fama da wata rashin lafiya lokacin da kike dauke da shi, irin su ciwon koda ko huhu, to ki guji yin tu’ammali da masu fama da cutar.

Yaya zan kare kaina daga cutar?

Ana yada cutar ne ta hanyar tari ko kuma idan mai dauke da ita ya taba wasu abubuwa irin su kofar da kowa ke tabawa da makamatansu.

Kula da lafiyar jiki da ta muhalli za ta taimaka wurin hana kamuwa da cutar:

 • Ku rufe hancinku da bakinku da kyalle idan kuka yi atishawa.
 • Ku jefar da tolifefa ko kyallen da kuka yi atishawa a ciki a kwandon zubar da shara
 • Ku wanke hannayenku da sabulu da ruwa akai-akai – ku yi amfan da sinadarin hand sanitiser idan ba ku samu ruwa ba
 • Ku guji hada jiki da mutanen da ba su da lafiya
 • Kada ku taba idanunku, ko hancinku ko bakinku idan baku tsaftace su ba

Ku rika motsa jiki a cikin gida ko a lambunanku ba tare da kun fita waje ba.

Shin muna iya yin amfani da takunkumin rufe fuska?

Gidauniyar masu fama da ciwon huhu ta Birtaniya ta ce bata bayar da shawarar yin amfani da takunkumin rufe fuska ba “domin babu wata shaida da ke nuna cewa yana da amfani.

Kazalika mutanen da ke fama da ciwon huhu ka iya fuskantar matsala wurin numfashi idan suka sanya takunkumin.”

Trending