Connect with us

Hausa

Italy: Dybala da Maldini sun kamu da Coronavirus

Published

on

Paulo Dybala

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dybala ne dan kwallon Juventus na uku da aka tabbatar ya kamu da Coronavirus

Dan kwallon Juventus da kuma Argentina Paulo Dybala ya kamu da cutar Coronavirus.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Dybala ya ce shi da buduwarsa duk suna dauke da cutar.

“Ni da Oriana muna da cutar, amma muna cikin yanayi me kyau” in ji Dybala mai shekara 26.

Shi ma tsohon kyaftin din Italiya, Paolo Maldini ya kamu da cutar.

Dybala ne dan kwallon Juve na uku da aka tabbatar ya kamu da Coronavirus bayan dan wasan baya Daniele Rugani da kuma Blaise Matuidi.

Tuni aka dakatar da gasar kwallon Italiya ta Serie A saboda cutar.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending