Connect with us

Hausa

Da kyar nake numfashi da na kamu da coronavirus — Duffy

Published

on

Lee Duffy

Hakkin mallakar hoto
Inpho

Kwana takwas Lee Duffy ya yi a asibiti kan na’urar da ke taimakawa yin numfashi kafin ya warke da coronavirus.

Tsohon dan wasan Warrenpoint da Newry City, mai shekara 28 ya ce tun farko baya iya yin numfashi da kansa, kuma ya firgita kan makomar rayuwarsa.

Daga baya aka gargade ni cewar ”Kar ka dauki lamarin da wasa abu ne mai girma”.

Kungiyar Warrenpoint ta yi wa Duffy fatan alheri da samun sauki cikin gaggawa ta kara da cewar cutar tana kama yara ko matasa ko kuma tsofaffi.

Duffy ya buga wasa a kungiyoyi da dama a Ireland sannan ya koma Newry mai buga Championship a watan Yulin a bara, bayan wata shida da ya yi a Warrenpoint.

Duffy ya ce ”Kamar yadda kowa ya sani na kamu da coronavirus mako biyu da suka wuce, na kuma samu sauki ina jin kwari sosai a jikina”.

Warrenpoint ta dauki Duffy daga Drogheda United, ya kuma taka leda a Shelbourne da Wexford da kuma Longford Town.

An dage dukkan wasannin gasar kwallon kafa ta cin kofin kasar Ireland har sai ranar 4 ga watan Afirilu.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending