Connect with us

Arewa

‘Yan Kannywood na jimami kan yadda mutuwa ta raba su da Ladi Mutu ka raba | BBC Hausa

Published

on

@saratudaso

Hakkin mallakar hoto
Mustapha Kaita

Image caption

.

A ranar Asabar ne aka samu labarin rasuwar fitacciyar ‘yar Kannywood din nan wato Ladi Mohammed wadda aka fi sani da Ladi Mutu ka raba.

An bayyana cewa jarumar dai ta rasu ne bayan ta yi fama da doguwar rashin lafiya.

Tuni jama’a da dama cikinsu har da ‘yan Kannywood suka fara yin ta’aziyya dangane da rasuwarta.

Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso kenan ke ta’aziyyar mutuwar Ladi a shafinta na Instagram.

Shi ma Ali Nuhu wanda tauraro ne a Kannywood ya yi ta’aziyyar rasuwarta a shafin instagram.

Saddiq Sani Saddiq ba a bar shi a baya ba wajen yin ta’aziyya kan rasuwar Marigayiya Ladi.

A bara ne dai bayan rashin lafiyar marigayiyar ta yi tsanani aka yi ta yawo da hotunanta a shafukan intanet inda ake cewa tana bukatar taimako.

Sai dai Marigayiyar ta fito ta kare kanta dangane da hakan inda ta ce masu son bata mata suna ne suka aikata hakan.

Tuni jama’a da dama cikinsu har da ‘yan Kannywood suka fara yin ta’aziyya dangane da rasuwarta.

Fim din da ta yi na Mutu ka raba na daga cikin fina-finan da suka sa ta yi fice kamar yadda Ibrahim Sheme ya shaida wa BBC da muka tuntube shi bayan rasuwarta.

Trending