Connect with us

Arewa

Sojojin Najeriya sun kona kauyuka a Borno

Published

on

Sojojin Najeriya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce, sojojin Najeriya sun kona wasu kauyuka tare da tursasa mazauna kauyukan barin muhallansu a wani martani na harin da aka kai baya-bayan nan.

Kungiyar ta ce ta samo wannan bayanin ne daga tattaunawar da ta yi da mazauna kauyukan da aka kona din.

Kungiyar ta ce sojojin sun kuma kama tare da tsare wasu maza shida ba tare da laifin komai ba daga kauyukan da ta konan.

Kungiyar ta Amnesty ta tattara dukkan bayananta a kan rikicin da ke faruwa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na tsawon shekara 10.

Amnesty ta ce, an hana mazan da aka tsaren magana da kowa kusan wata guda tare da azabtar da su har sai da aka sake su a ranar 30 ga watan Janairun 2020.

  • Buhari ya mayar da martani kan ihu da aka yi masa a Maiduguri
  • Ndume ya roki Buhari ya kawo karshen rikicin Boko Haram

Daraktan kungiyar a Najeriya, Osai Ojigho, ya ce “Ya kamata a bincike sosai a kan abin da ya faru a game da kona kauyukan da kuma tursasawa mazauna yankunan barin gidajensu ba tare da laifin komai ba”.

Daraktan ya ce “Mun jima muna nanata irin cin zarafin da sojojin Najeriya ke yi wa fararen hula, amma ba a dauki matakin komai ba, don haka ya kamata a bincika a yi wa wadanda aka zalinta adalci”.

Tun daga watan Disambar da ya gabata, Boko Haram ta kara zafafa hare-harenta a yankin arewa maso gabashin Najeriya, musammam ma a hanyoyin zuwa Maiduguri da Damaturu.

To sai dai kuma a cikin wasu bincike da Amnesty ta yi a baya-bayan nan ta gano cewa sojoji na amfani da wasu dabaru na rashin bin ka’ida, inda suke huce haushinsu a kan fararen hula abin da kungiyar ta ce zai zama laifin yaki.

Hakkin mallakar hoto
Wikipidia

Kungiyar ta Amnesty ta samu tattaunawa da mata 12 da kuma wasu maza daga cikin wadanda aka tursasawa barin muhallansu a ranar 3 da 4 ga watan Janairun da ya wuce.

Hotunan da aka samu daga tauraron garuruwan Bukarti da Ngariri da kuma Matiri, sun nuna yadda aka kona komai a garuruwan, haka hotunan sun nuna yadda aka kona wasu kauyukan da ke makwabtaka da wadannan garuruwan.

Wasu da aka kona wa garuruwa sun shida wa Amnesty cewa, da misalin karfe 3 na yammacin ranar 3 ga watan Janairun 2020 ne, sojoji suka bukaci mazauna kauyukan da su fice su je kan hanya su jira, daga nan sai aka ce musu su shiga cikin wasu manyan motoci, bayan nan ne sai sojojin suka koma kauyen Bukarti suka kona.

Ganau din suka ce “Muna gani aka kona mana gidaje ga shi ba dauki komai namu ba”.

Ganau din sun ce, an tafi da mata da yara da kuma maza da dama a cikin manyan motocin da sojojin suka kawo inda aka kai su sansanin ‘yan gudun hijra da ke kusa da Maiduguri.

Haka sojojin washe gari ma ranar 4 ga watan Janairun 2020, sojojin suka je kauyen Ngariri da makwabtansa suka kona suka kuma kwashe mutanen kauyen zuwa sansanin ‘yan gudun hijra.

Mazauna kauyukan, sun shaida wa Amnesty cewa, an lalata dukkan amfanin gonarsu sannan an kashe musu dabbobi.

Matashiya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kalla mutum 27,000 ne suka rasa rayukansu a tsawon shekara 10 na rikicin Boko Haram a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.

A watan Yulin 2019 ne aka cika shekara 10 da kashe Shugaban kungiyar Boko Haram na farko Muhammad Yusuf.

Gwamnatin Buhari dai ta dade tana ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin arewa maso gabas, amma kuma har yanzu mayakan kungiyar na ci gaba da yi wa mutanen yankin barazana.

Harin da aka kai Auno ya fusata mutanen Borno, inda da dama suka zargi jami’an tsaro da sakaci bayan sun rufe hanyar shiga Maiduguri da yammaci, dalilin da ya sa mayakan Boko Haram suka riske matafiya a cikin dare.

Trending