Connect with us

Hausa

Ronaldo ya ci kwallo a wasa na tara a jere a Serie A | BBC Hausa

Published

on

Ronaldo

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Cristiano Ronaldo ne ya ci kwallo biyu a wasan gasar Serie A da Juventus ta doke Fioentina 3-0 ranar Lahadi.

Kawo yanzu tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid ya ci kwallo 10 a wasa shida baya da ya buga wa Juve.

Juventus wadda ta karbi bakuncin Fiorentina ta samu bugun fenariti, kuma Ronaldo ne ya buga ya kuma ci.

Can karshen lokacin da za a yi hutu ne aka yi wa dan wasan Juventus, Rodrigo Bentancur keta a da’ira ta 18, kuma Ronaldo ne ya kara buga wa ya kuma ci na biyu.

Kawo yanzu Ronaldo, ya ci kwallo a wasa na tara a jere a Serie A, kuma dan kwallo na farko da ya yi haka a Juventus, tun bayan David Trezeguet da ya yi bajintar a 2005.

Dan wasan na tawagar Portugal ya ci kwallo 50 a wasa 70 tun komawarsa Italiya da taka leda daga Real Madrid a 2018.

Nasarar da Juventus ta yi ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Serie A da maki 50, bayan wasa mako na 22 da tazarar maki shida tsakaninta da Inter Milan ta biyu a teburi.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending