Connect with us

Hausa

Amurka ta kori Sojojin Saudiyya da ke daukar horo

Published

on

The attack last month occurred at the Naval Air Station Pensacola, Florida

Harin sansanin sojin Pensacola a Florida watan jiya ne ya sa aka kori sojojin

Amurka ta kori sojin Saudiyya ashirin da daya bayan wani hari da wani jami’in sojin Saudiyya ya kai wani sansani a watan da ya gabata.

Ba a tuhume su game da taimakawa matashin wanda laftanal ne a rundunar sojin saman Saudiyya ba.

Amma babban lauyan gwamnatin Amurka William Barr ya ce an gano suna dauke da wasu bayanai da ke da alaka da kaifin kishin jihadi da kuma wasu hotuna masu tayar da hankali.

Ma’aikatan jirgin ruwan soji uku sun mutu yayin da takwas suka jikkata a harin 6 ga Disamba.

Bayan faruwar lamarin ne kuma aka dakatar da horar da jami’an tsaron Saudiyya a Amurka.

Mista Barr ya fadawa wani taron manema labarai a ranar Litinin cewa harbin na ta’addanci ne.

Ya ce ya nemi kamfanin kera wayoyi na Apple ya bude wayar jami’in da ya bude wutar, duk da cewa ya harbi wayar amma jami’an hukumar tsaron kasar ta FBI sun tashe ta, kuma ana iya samun wasu bayanai masu muhimmanci a cikinta.


An kwashe gawarwakin matuka jirgin ruwan da suka mutu zuwa sansanin sojin sama na Dover da ke Delaware

Tashar Jiragen saman ta Pensacola ta jima a matsayin wurin horar da jami’an tsaron kasashen waje game da sanin makamar aiki, kuma matuka jiragen yakin sojin saman Saudiyya sun fara daukar horo a wurin tun a shekarar 1995, da sauran sojin saman kasashen Italiya, da Singapore, da Jamus.

Bayan faruwar lamarin a watan da ya gabata, babban kwamandan sansanin ya ce jami’an dari biyu kacal aka karba a sansanin don ba su horo, a maimakon dubu goma sha shidda da aka saba ba dama a baya.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending