Connect with us

Hausa

Real ta yi zawarcin Mourinho, Wai Rakitic zai koma Juve? | BBC Hausa

Published

on

Hakkin mallakar hoto
PA Media

Real Madrid ta so ta biya Maurinho fam miliyan 12 domin ya jira idan ya gama aikinsa ya karba ba tare da ya karbi aiki a wata kungiya ba. (Sun)

Inter Milan za ta nemi dan wasan gaban Arsenal Pierre Emerick Aubameyang mai shekaru 30 a watan Janairu. (Star)

Dan wasan Liverpool Coutinho da ke zaman aro a Bayern Munich ya ce yana fatan ya cigaba da zama a kungiyar. (Marca)

Liverpool da Manchester City har ma da Manchester United na neman matsahin dan wasan Faransa Mathis Cherki mai shekaru 16 da ke wasa a Lyon. (90 min)

Juventus ta musanta rahotannin da ke cewa za ta sayi dan wasan tsakiyar Barcelona Ivan Rakitic mai shekaru 31. (Mail).

Barcelona za ta iya neman dan wasan tsakiyar Borussia Dortmund Julian Weigl a kan gam miliyan 21. (Mail)

Trending