Connect with us

Hausa

Brendan Rodgers ya yi watsi da batun barin Leicester zuwa Arsenal

Published

on

James Meddisson daga hagu tare da Brendan Rodgers

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

James Meddisson daga hagu tare da Brendan Rodgers

Kocin Leicester Brendan Rodgers ya yi watsi da jita-jitar da ke danganta shi da komawa kocin Arsenal.

Kocin wanda dan kasar arewacin Ireland, mai shekara 46, ya jagoranci kungiyar Foxes zuwa mataki na biyu a gasar Premier kuma dan takara ne wanda ke neman maye gurbin Unai Emery wanda aka kora a makon da ya gabata.

A baya dai Rodgers ya yarda cewa akwai batun barin kungiyar, idan kwantaraginsa ya kare amma ya ce: “Me zai sa zan bar Leicester City a wannan lokacin?

“Ina matukar farin ciki don haka ba za a bukaci neman wani wuri ba.”

An nada tsohon kocin na Liverpool da Celtic ne a Leicester a watan Fabrairu kuma bayan ya kare a mataki na tara a bara, ya kai kungiyarsa ta lashe wasanni 10 daga cikin wasannin 14 na bana.

Arsenal ta kori Emery bayan watanni 18 da fara aiki a lokacin da suka yi rashin nasara a wasanni da dama a jere, wanda rabon da suka yi haka tun shekarar 1992.

Gunners wacce ke matsayi na takwas a teburi, tana bayan Leicester, inda ta sanya tsohon dan wasanta Freddie Ljungberg jagorantar ‘yan wasanta na wucin gadi.

Rodgers ya ce game da jita-jitar da ake yadawa mai alaka da matsayina a Emirates: “Ina da kwangila daga nan har zuwa 2022. Har yanzu, na san manajoji suna rasa aikinsu, kulob dina bai nuna min cewa za su kore ni ba.

“Ina aiki tare da gungun ‘yan wasan da ke da kwarewa. Na ba da amsar da ta dace.

“A gare ni, ina sake maimaitawa, ina cikin farin ciki a nan. Ina matukar farin ciki a nan. Ina jin ina so na ci gaba da hakan.”

Trending