Connect with us

Buhari

Abubuwa 10 kan Jami’ar Sufuri ta Daura a Najeriya | BBC Hausa

Published

on

A

Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya assasa harsashin gina Jami’ar Sufuri ta farko a kasar.

Za a gina makarantar ne a mahaifar shugaban da ke Daura a jihar Katsina, arewacin Najeriya.

Ga dai wasu abubuwa 10 da kuke bukatar sani kan wannan sabuwar makaranta:

  1. A watan Oktoban 2018 gwamnatin tarayya ta amince da fitar da kudin da za a gina jami’ar, a cewar Hukumar da ke Kula da Jami’o’i ta Najeriya NUC.
  2. Jami’ar Sufurin za ta mayar da hankali ne kan bincike da ci gaban bangaren sufuri a Najeriya.
  3. Wannan makaranta ta gwamnatin tarayya ce, sannan kuma za a bude wata irinta a jihar Ribas da ke kudancin Najeriya, a garinsu Ministan Sufuri Chibuike Amaechi.
  4. Za a kashe dala miliyan 50 wajen gina jami’ar (naira biliyan 18), kamar yadda Amaechi ya fada.
  5. Kamfanin gine-gine na kasar China CCECC ne zai gina makarantar.
  6. Dalilin gina makarantar shi ne don a cike gibin rashin aikin yi a bangaren sufuri, kamar yadda Amaechi ya ce.
  7. Sannan kuma gwamnatin tarayya na son horas da mutanen da za su dinga kula da layukan dogo na kasar kamar yadda ake yi wa na titunan mota.
  8. A yanzu haka akwai daliban Najeriya da dama da ke karatun abin da ya shafi harkar layin dogo a China. Ana sa rana za su koma Najeriya don taka rawa a matsayin masu bincike a jami’ar idan ta fara aiki.
  9. Matasan kasar da gwamnati ta tura China don karanta fannin injiniya na layin dogo ne za su fara koyarwa a makarantar kafin su fara wani aikin.
  10. Ana sa rana a shekarar 2020 za a fara karatu a makarantar.

Hakkin mallakar hoto
@toluogunlesi/Twitter

Image caption

Matasan kasar da gwamnati ta tura China don karanta fannin injiniya na layin dogo ne za su fara koyarwa a makarantar kafin su fara wani aikin

Bangaren sufuri na daga cikin wadanda gwamnatin Najeriya ta fi mayar da hankali a kansu tun bayan da Shugaba Buhari ya fara mulki a 2015, musamman kan yadda ake kara gina layukam dogo da kuma gyara filayen jiragen saman kasar.

Gwamnatin Buharin ta ranto kudade da dama daga China, wadda ke kan gaba wajen zuba jari a harkar layukan dogo a Najeriya.

Trending