Connect with us

Hausa

Arsenal: Rogers ko Arteta na iya maye gurbin Emery

Published

on

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Watford za ta yi zama ranar Lahadi da nufin bayyana sallamar mai horar da ‘yan wasanta Quique Sanchez Flores a karo na biyu. (The Athletic)

Tsohon mai horar da ‘yan wasan Tottenham Mauricio Pochettino wanda rahotanni su ka ce Arsenal da Manchester United na nema zai biya miliyan 12.5 idan har ya karbi aiki a wata kungiya da ke gasar firimiya a kakar da ake ciki. (Sunday Express)

A wata mai kama da haka abokan Pochettino sun shawarce shi da kada ya kuskura ya karbi horar da Arsenal. Sun shawarce shi da ya jira aiki mai gwa’bi. (Sunday Telegraph)

An bayyana sunayen mai horar da ‘yan wasan Leicester Brendan Rodgers da tsohon dan wasan Arsenal Mikel Arteta a cikin jerin wadanda ake tunanin su maye gurbin Unai Emery. (Star on Sunday)

Real Madrid za ta taya dan wasan gaba na Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang mai shekaru 30, kan kudi fam miliyan 70, kuma za a saka dan wasanta na tsakiya James Rodriguez mai shekaru 28 cikin cinikin. (Eldesmarque, ta hannun Star)

Liverpool da Tottenham na rububin sayen dan wasan tsakiya na Lyon da kasar Holland mai shekara 25 Memphis Depay. (Sunday Express)

Golan Ingila Jordan Pickford ya ce ‘yan wasan Everton na goyon bayan mai horar da su Marco Silva, kuma ba sa maraba da shirin sallamarsa. (Observer)

Aston Villa na shirin sayar da dan wasan gaba na Ivory Coast Kodjia a watan Janairu. (Football Insider).

Chelsea na sa ido kan Zaha na Crystal Palace da kuma Jadon Sancho na Borussia Dortmund, dan wasa mai shekara 19 a kokarin kungiyar na karawa gabanta karfi. (Sunday Express).

A wata mai kama da haka Juventus na da sha’awar sayen dan wasan baya na Chelsea Emerson Palmeiri mai shekara 25. (Calciomercato)

Trending