Connect with us

Hausa

Buhari ya kulla yarjejeniya da Iran

Published

on

Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau

Najeriya da Iran sun amince su kulla kawance a fannin amfani da iskar gas da kasuwanci da zuba jari da kuma inganta harakar noma da fasaha.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaba Buhari da mataimakin shugaban Iran sun amince su kulla kawance ne yayin taron kasashe masu arzikin iskar gas da aka gudanar a Equatorial Guinea.

Ya ce shugabannin sun kuma amince su kafa hukuma ta hadin guiwa da za ta tabbatar da yarjejeniyar.

Mataimakin Shugaban Iran Mohammad Nahavandian ya jaddada cewa akwai abubuwa da dama da Iran da Najeriya za su iya samarwa saboda baiwar da Allah ya ba su. yayin da shugaba Buhari ya bayyana fatan Najeriya za ta kai matsayin Iran a arzikin iskar Gas.

Sannan Iran ta yi tayin taimakawa Najeriya wajen yakar ta’addanci, inda ta bayar da misali da yadda yaki da ISIS a Iraqi da Syria ya kasance muhimmin aiki ga yakar ta’addanci a duniya.

Shugaba Buhari ya yaba da abin da ya ce Iran ta yi nasarar yaki da ISIS a Iraqi da Syria, inda ya ce kwace rijiyoyin mai da daga hannun yan ta”adda ya dakile hanyar da suke samu wajen tallawa Boko Haram a yankin tafkin chadi.

Trending