Connect with us

Hausa

Bijirewar Iran na damun Tarayyar Turai

Published

on

Iranians hold national flag and a picture of Ayatollah Khamenei (file photo)

A sama-sama ana iya cewa Iran na janyewa daga yarjejeniyar nan ta 2015 kan samar da makamashin nukiliyar kasar.

A jiya Talata hukumar IAEA mai sa ido kan yaduwar makaman nukiliya ta sanar cewa Iran ta tara kimanin sinadarin Uranium da yawansa ya nunka wanda aka amince ma ta tarawa har sau goma sha hudu.

Ban da wannan batun ma, Iran ta ta kuma aiwatar da wani kashedi da ta yi cewa za ta jinginar da hadin kan da ta ke bayar wa ga masu binciken MDD su ci gaba da kai ziyarar ba-zata z cibiyoyin binciken nata.

Birtaniya da Faransa da Jamus duka sun soki matakin na Iran, suna cea zai kara nisanta kasar daga matsayar da ka amince ta tsaya na yarjejeniyar ta 2015.

Amma akwai wasu alamu ma su karfafa gwuiwa ga kasashen na Turai a bangaren diflomasiyya.

Ministan harkokin wajen na Iran, Javad Zarif ya sanar da shirin kasar na komawa bisa teburin tattaunawa da Amurka nan ba da jimawa ba – wanda shi ne karon farko da hakan zai faru cikin shekara hudu, kuma wannan ganawar na cikin abubuwanda TT ke kokarin tabbatar wa an yi cikin watanni masu zuwa.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending