BBC ta bude gasar rubutu a harshen Pidgin | BBC Hausa

Wani likita yana rubutu da biro kan takarda

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Za a lashe kyautar sama da naira 180,000

Sashen Turancin broka wato BBC Pidgin ya kaddamar da gasar rubutun zube da harshen Pidgin a ranar Alhamis 1 ga watan Agustan 2019.

Gasar a bude take ga dukkanin daliban manyan makarantun gaba da sakandare a nahiyar Afirka.

Masu sha’awar shiga gasar za su rubuta makala ne mai kalmomin da ba su wuce 800 ba kan maudu’in “ko mace za ta iya jagorancin siyasa a nahiyar Afirka?” (“Is Africa ready for female political leadership?”).

Wani rukunin alkalai da suka hada da malamai da ‘yan jarida da marubuta na harshen Pidgin wadanda suka fito daga Afirka ta Yamma ne za su zabi mutum daya wanda ya yi nasara.

Wajibi ne kowacce makala ta dace da tsarin harshen Pidgin tare da bin ka’idojin rubutu.

Za a sanar da wanda ya yi nasarar ne a Legas ranar 20 ga watan Satumban 2019. Sannan za a ba shi kyautar dala $500 (kusan naira 180,000)

Za a rufe shiga gasar ne a ranar Juma’a 30 ga watan Agustan 2019.

A aiko da makala zuwa adireshin imel na bbcpidgin.essay@bbc.co.uk

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...