
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta doke Fulham 3-0 a wasan mako na 27 a gasar Premier League ranar Lahadi a Craven Cotage.
Arsenal ta fara cin kwallo ta hannun ta hannun Gabriel Magalhaes aminti na 21 da fara wasa, sanan minti biyar tsakani ta kara na biyu ta hannun Gabriel Martinelli.
Daf da za a yi hutu ne Gunners ta kara na uku ta hannun kyaftin dinta, Martin Odegaard.
Ranar 27 ga watan Agustan 2022, Arsenal ta doke Fulham 2-1 a Emirates a wasan farko a babbar gasar tamaula ta Ingila da suka buga a bana.
Arsenal za ta kara a wasan gaba da Sporting a Emirates a fafatawa ta biyu a ‘yan 16 a Europa League.
Ranar 9 ga watan Maris Gunners ta tashi 2-2 a gidan Sporting a wasan farko a gasar ta Europa ta kakar nan.
Daga nan kuma Arsenal za ta karbi bakuncin Crystal Palace a Premier League a wasan mako na 28 ranar 19 ga watan Maris.
Ita kuwa Fulham za ta fafata da Manchester United a daf da na kusa da na karshe a FA Cup ranar 19 ga watan Maris.