[ad_1]
Shugaban kasa, Muhammad Buhari a ranar Talata ya gana da babban sifetan ‘yansanda, Ibrahim Idris a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ganawar ta su na zuwa ne kwana guda bayan da rundunar Æ´ansandan Najeriya ta gayyaci shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki.
Acewar rundunar akwai tambayoyi da yakamata shugaban majalisar dattawan ya amsa game da fashin da aka yi a garin Offa dake jihar.
Tuni Saraki ya musalta zargin da ake masa na alaka da mutanen da suka aikata fashin.
Idris bai yi magana da yan jaridun dake fadar shugaban kasa ba bayan ganawar tasu.
Koda a safiyar yau sai da wata tawagar jami’an ƴan sanda suka tare ayarin motocin shugaban majalisar dattawan inda suka yi wa gidansa kawanya.
[ad_2]