Ba mu kama Yari saboda ya ƙi ɗaukan kiran wayar Tinubu ba—DSS

A yau Lahadin ne jami’an farin kaya na DSS suka musanta cewa sun kama Sanata Abdulaziz Yari ne saboda ya ki amsa kiran wayar shugaban kasa Bola Tinubu.

Kakakin hukumar DSS, Dr Peter Afunanya, ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Sanarwar da aka wallafa a shafin Twitter na hukumar ta DSS ta bayyana ikirarin a matsayin abin dariya

Da yake tabbatar da cewa DSS ne ta gayyaci Yari, Afunanya a cikin sanarwar ya ce Sanatan ya san dalilin gayyatar sa.

Ya kuma musanta zargin da ake yi wa hukumar na yi wa alkalan kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa zagon kasa.

More from this stream

Recomended