Atiku Ya Lissafo Sunayen Masu Cin Hanci Guda 30 Da Ke Cikin Gwamnatin Buhari

Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, ya lissafa ‘gurbatattun’ mutane 30 da ke aiki wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Mai taimakawa na musamman a fanin watsa labarai, Phrank Shu’aibu ne ya fitar da jerin sunayen a jiya Lahadi kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito. Ya lura cewa wasu daga cikinsu ‘yan jam’iyyar APC ne yayin da sauran kuma sun shiga jam’iyyar ne domin su tsira daga binciken aikata rashawa. Atiku ya lissafa gurbatattun mutane 30 a cikin gwamnatin Buhari

Ya lissafo jiga-jigai a jam’iyyar APC kamar tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran APC na kasa, Bola Tinubu; Shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari, Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan Nasarawa, Abdullahi Adamu; Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal; Shugaban hukumar NTDC, Folarin Coker; Ministan Sadarwa, Lai Mohammed.

Cikin jerin sunayen akwai hafsin sojin Najeriya, Laftanat Tukur Buratai; Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika; Mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari; Shugaban hukumar tace fina-finai na kasa, Adedayo Thomas; Tsohon gwamnan Bauchi, Adamu Mu’azu; Tsohon gwamnan jihar Osun, Iyiola Omisore; Tsohon shugaban hukumar Fansho na kasa, Abdulrashin Maina; Tsohon karamin Ministan Tsaro, Musliu Obanikoro da Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu.

Saura sun hada da Gwaman Bauchi, Isah Yuguda; Sanata Godswill Akpabio; Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbanjo; Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje; Tsohon gwamna jihar Jigawa, Saminu Turaki, Sakataren BCDA kuma surukin Buhari, Junaid Abdullahi; tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Wamako; Dan takarar gwamnan APC na jihar Imo, Hope Uzodinma, Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi da gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

Har ila yau, sauran wadanda aka ambaci sunayensu su ne, Shugaban hukumar NNPC, Maikanti Baru da Shugaban hukumar tattara bayannan sirri na kasa (NIA) da aka dakatar, Ayodele Oke.

t

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...