Connect with us

Entertainment

Kannywood: Mutanen da ke jan akalar Arewacin Najeriya a fannin nishadi

Published

on

Mutanen da ke jan akalar Arewacin Najeriya a fannin nishadi

A shekarun baya-bayan nan, an ga wani sauyi ko sabon salo a tsarin fina-finan Kannywood, wato shirye shirye na dogon zango ko series.

Asali yadda aka sani, a kan yi fim a kasa shi gida daya ko biyu wani lokaci har zuwa uku.

Sai ga shi masu shirya fina-finan sun bullo da wani sabon salon yin fim wanda za a kwashe wata da watanni ana nuna shi wato duk mako a kan saki sabon bangare, ko kuma episode.

Sannan a kan raba fina-finan ne zango-zango.

Wannan salon ya yi matukar samun karbuwa.

Zai yi wahala ka ga taron mata, kai ma da maza musamman matasa na Hausawa ba ka ji an ambato shirin Gidan Badamasi ba, ko Dadin Kowa ko Labarina.

Ana iya cewa ma yadda mutane ke ambato taurarin wadannan shirye-shirye, kai ka rantse ‘yan uwansu ne ko abokansu.

Har sabbin karin magana aka samar daga fina-finan a maganganun mutane na yau da kullum saboda tasirin da suka yi

Sai ka ji an ce “Wane talauci kamar Kamaye” ko a ce “Kar dai ka zama mayaudari fa irin Mahmud din Sumayya.”

Haka ma a shafukan sada zumunta.

Wannan na nuna yadda masu kallo ke nishadantuwa da samun nutsuwa yayin kallon fina-finan.

An san cewa duk wani abu da ya samu karbuwa irin wannan, dole ne akwai mutane a bayan fage da suka dage wajen ganin ya yi fice.

Wannan makalar za ta duba mutanen da ke shirya fina-finai na dogon zango na Dadin Kowa da Kwana Casa’in da Gidan Badamasi da Labarina.

Salisu T Balarabe – Shirin Dadin Kowa da Shirin Kwana Casa’in

Salisu T Balarabe shi ne jagoran shirye shiryen Dadin Kowa da Kwana Casa’in da ake nuna a tashar Arewa 24 da ke tauraron dan Adam.

A kan nuna sabon shirin Dadin Kowa duk ranar Asabar da karfe 8 na dare, Kwana Casa’in kuma duk ranar Lahadi da karfe 8 na dare.

Shi ne shugaban kamfanin ACCUTZ Media mai shirya fina-finai.

Salisu ya yi karatu mai zurfi a bangaren shirya fim, sannan yana da kwarewa a aikin jarida da rubutu da harkar komfuta.

Ya taba rike mukamin mataimakin shugaban Kungiyar Masu Tace Hoto ta Arewa (GAVE) sannan ya yi sakataren Kungiyar Masu Tace Hoto ta MPEG.

Ya karbi lambobin yabo a gida Najeriya da kuma waje.

Salisu ya shirya fina-finai da dama a Kannywood kamar Taron Dangi da Gantali da Zo Muje da Halimatus Sadiya da Sansanin Tuarari da dai sauransu, kuma duka wadannan ba fina-finai ne na dogon zango ba.

Ya ce an fara haska shirin Dadin Kowa ne a shekarar 2014, kuma shiri ne da ke hasko zamantakewa ta yau da kullum a rayuwar al’ummar Najeriya musamman a arewacin kasar masu karamin karfi.

“Wannan shirin an tsara shi ne don ya duba yadda masu karamin karfi ke rayuwa a arewacin Najeriya, ba tare da an duba bambancin yare ko kabilanci ko addini ba,” a cewar Salisu.

“Shi ya sa ma idan aka duba shirin ba kasafai a ke nuna birni ba. Kusan komai a kauye a ke nunawa,” in ji shi.

Shirin na duba al’amuran da suka fi damun al’umma kamar ta’addanci da tu’ammali da miyagun kwayoyi da zaman aure da almajirci da talauci da cin hanci da rashawa da garkuwa da mutane don kudin fansa da dai sauransu.

Kawo yanzu, shirin Dadin Kowa na da episode sama da 250 idan aka hada duka bangarorin shirin da suka hada da Dadin Kowa da Dadin Kowa Sabon Salo da Dadin Kowa Wasa farin Girki.

Salisu T Balarabe ya ce an kirkiri Shirin Kwana Casa’in ne musamman don a duba matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya.

“Mutane da dama kan yi tunanin shirin siyasa ne kawai amma asali abun da shirin ke so ya nuna shi ne yadda cin hanci da rashawa ya yi katutu, kuma a nazarin da aka yi sai muka ga wannan matsalar ta fi yawa a bangaren wutar lantarki da ilimi da kiwon lafiya.

“Sai muke kokarin samar da mafita ta hanyar kirkirar labaran da ke cikin wannan shirin,” a cewarsa.

Falalu Dorayi – Shirin Gidan Badamasi

Falalu Abubakar Dorayi shi ne shugaban kamfanin Dorayi Films and Distribution Limited da ke shirye fim din Gidan Badamasi a tashar nan ta tauraron dan Adam ta Arewa 24 duk ranar Alhamis.

Falalu ya fara harkar fim ne a shekarar 1997 bayan kammala karatunsa na sakandire.

Dorayi na daya daga cikin manyan masu shirya fina-finai a Kannywood, kuma a wasu lokutan ma ya ba da umarni sannan ya kan fito a dan wasa.

A shekarar 2019 ne ya fara bayar da umarni kuma ya fara fitowa a fim mai dogon zango na Gidan Badamasi.

Gidan Badamasi dai a iya cewa shiri ne na barkwanci wanda ke nuna iyalin wani mai dukiya, Alhaji Badamasi mai tarin ‘ya’ya.

Shirin Gidan Badamasi ya hasko rayuwar wadannan ‘ya’ya nasa da ke da mabambantan halaye amma dukkansu ke da buri guda- mahaifinsu ya rasu sun gaji dimbin dukiyar da ya tara.

Falalu Dorayi ya ce ya kirkiri shirin Gidan Badamasi ne saboda yadda ya ga an yi wa bangaren barkwanci a masana’antar Kannywood “rikon sakainar kashi.”

“A baya fina-finai na sun fi mayar da hankali kan zamantakewa da laifuka. Sai na ga bangaren barkwanci kuwa sai a ce an nadi fim a ‘yan kwanaki shi ya sa na sauya akalata”, in ji Falalu.

Wannan sauyin da ya yi ya haifar da fina-finai barkwanci kamar Ibro Dan Fulani da Hotiho da Ibro Dan Magori da Namamajo da dai sauransu wanda duk shi ne ya shirya su.

Falalu ya ce “shi ya sa ko da aka gayyace ni in fara shirya fim mai dogon zango kawai na tsunduma banagren barkwanci kuma na samar da Gidan Badamasi don na fi yarda da irinsu.”

Ya ce yana cikin mutanen da suka sauya akalar fina-finan Ibro da aka fi sani a baya da ‘camama’.

Falalu marubuci ne kuma ya ce ya shirya fina-finai sama da dari kawo yanzu.

Haka kuma, ya lashe lambar yabo ta mai ba da umarnin da ya fi kowanne kwarewa a kalla sau biyar.

Falalu Dorayi ya sha hada kai da manyan hukumomi wajen shirya fina-finai, kamar hukumar UNICEF don wayar da kan al’umma a arewacin Najeriya kan matsalolin shayarwa da yin bahaya a bainar jama’a da cutar shan Inna da dai sauransu.

Aminu Saira – Shirin Labarina

Aminu Muhammad Ahmad wanda aka fi sani da Aminu Saira shaharraren mai ba da umarni kuma mai shirya fina-finai ne a Kannywood.

Aminu ne shugaban kamfanin Saira Movies kuma shi ne jagoran shirin Labarina da ake nuna wa a tashar Arewa 24 duk ranar Litinin da karfe 8 na dare.

Ya fara bayar da umarni ne a Kannywood a shekarar 2006 da fim dinsa mai suna Musnadi.

Ya rubuta kuma ya bayar da umarnin fina-finai da dama kamar Jamila da Jamilu da Ashabul Kahafi da Ga Duhu Ga Haske da Maryam Diyana da Dare Da Yawa da Rai da Rai ddai sauransu.

Aminu dan uwane ga mawaka Misbahu M Ahmad da Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin waka.

Aminu ya samu lambobin yabo da dama a harkar shira fim inda a shekarar 2014 ya lashe lambar yabo na bayar da umarni na Jurors Choice Awards.

Saira ya bayyana cewa ya fara shirin Labarina bayan da ya yi la’akari da yadda hankalin masu bibiyar fina-finan Hausa ya fara karkata kan shirye-shirye na dogon zango na Indiya da Turkiyya da Koriya.

“Sai na fahimci idan ba mu tashi tsaye mun kirkiri wani abu makamantan wadannan fina-finan ba, za a bar mu a baya.”

“A lokacin ne na zauna da abokin aikina Nazifi Asnanic muka fara aiki kan Labarina,” a cewar Saira.

Ya bayyana cewa burinsa shi ne ya fitar da sakonnin juriya da hakuri da kai zuciya nesa da illar nuna zalama a wannan shiri.

Aminu Saira ya ce yana alfahari da karbuwar da shirin Labarina ya samu sosai duk da cewa ya kunshi soyayya amma “sai ka ga manyan mutane maza daga ko wane bangare” suna bibiyar shirin.

Aminu Saira na daya daga cikin masu ba da umarni mafiya tsada a Kannywood.

A shekarar 2016 ne aka bayyana Aminu Saira a matsayin mai ba da umarnin da ya fi ko wanne a masana’antar.

(BBC Hausa)

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending