Connect with us

Hausa

Donald Trump da mataimakinsa sun raba gari kan Joe Biden

Published

on

Trump

An tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasar mai barin gado, Mike Pence ya ce shi zai halarci wajen bikin rantsar da zababben shugaban kasar, Joe Biden.

Tabbacin na zuwa ne kwana guda bayan mataimakin ya juya wa mai gidansa Donald Trump baya, ta hanyar amincewa da nasarar Joe Biden a zaben shugaban kasar.

An dai ce shugaba mai jiran gado, Joe Biden ne ya aike da takardar gayyata ga mista Pence inda kuma ya ce zai karrama wannan gayyata ya halarta.

Mr Trump dai ya ce shi kam ba zai halarci bikin rantsuwar ba, wani abu da ya saba wa dadaddiyar al’adar shugabannin kasar masu barin gado.

Ana ganin alaka ta yi tsami tsakanin shugaban da mataimakinsa tun bayan da mista Pence ya ki yin amfani da damar da yake da ita wajen yin cikas ga tabbatar da nasarar Joe Biden a majalisar dattawa ranar Laraba.

To sai dai za a iya cewa wannan ne karon farko da aka ga mutanen biyu sun samu ra’ayoyin da suka sha banban da juna kasancewar shekaru hudu a tsawon shugabancinsu ba a taba jin wani makamancin hakan ba.

Tuni dai ‘yayan jam’iyyar Democrats a majalisar wakilan kasar suka ce za su fara shirin tsige shugaba Trump a gobe Litinin, bayan sun zarge shi da tunzura magoya bayansa domin yin kutse a ginin majalisar da ke Washington.

Za a iya cewa ba a taba samun shugaban da ke cike da takaddama a Amurka ba kamar Donald Trump wanda ya angiza magoya bayansa kutsawa ginin majalisar dokokin kasar domin tayar da yamutsi saboda ya fadi zabe.

Yanzu haka dai Donald Trump ya zama saniyar ware a duniya kuma akwai alamun da ke nuna zai iya fuskar abin da ya fi haka bayan mulkinsa.

Ko a ranar Lahadi sai da kamfanin Twitter da sauran kafofin sada zumunta suka sanar da toshe shafinsa har abada.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending