Connect with us

Hausa

Kasuwar cinikin ‘yan ƙwallon ƙafa: Makomar Skriniar, Schuurs, Pochettino, Zidane, Hazard, Moyes, Williams

Published

on

Zinedine Zidane

A shirye Inter Milan ta ke ta sayar da Milan Skriniar, dan wasanta na baya mai shekara 25 ga Tottehnam kan fam miliyan 45 a watan gobe. (Sun)

Ana hasashe cewa Perr Schuurs, dan wasan baya na kasar Netherlands mai shekara 22 zai koma Liverpool, amma shi ya ce bai shirya barin Ajax ba tukuna. (Mirror)

Tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino na kan gaban koci Raul na Real Madrid wajen wanda zai maye gurbin Zinedine Zidane idan Real ta sallami kocin nata dan kasar Faransa. (Marca)

Sai dai ana hasashen Pochettino yafi son tafiya Paris St-Germain inda ake sa ran zai mayegurbin Thomas Tuchel. (Talksport)

Zidane ba shi da karfin gwuiwa wasu ‘yan wasan da ya ke horaswa za su iya tsirar da kungiyar. ‘Yan wasan sun hada da Eden Hazard, dan kasar Netherlands mai shekara 29. (Sport)

A halin yanzu Zidane na da goyon bayan shugabannin kungiyar Real Madrid har da ‘yan wasan kungiyar, amma wasanni kuk masu zuwa ne za su nuna idan zai ci gaba da zama a kungiyar ko za a sallame shi. (ESPN)

West Ham na tattaunawa da kocinta David Moyes domin ya tsawaita zamansa a kungiyar, domin wa’adin kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa na bana. (Sky Sports)

Newcastle ta dade tana sa ido kan dan wasan Manchester United Brandon Williams mai shekara 20 da haihuwa kuma dan wasan baya na Ingila. (Newcastle Chronicle)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce shi da daraktan wasanni Edu na shirye-shiryen sayo wasu ‘yan wasa da zarar an bude kasuwa a watan Janairu mai zuwa. (London Evening Standard)

Leicester na iya sake duba yiwuwar sayo Wiliam Carvalho dan waasan tsakiya na Portugal mai shekara 28 domin Real Betis na son sayar da shi a watan Janairu. (La Razon, via Leicester Mercury)

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending